An ƙara wa manyan hafsoshi Soji 122 ƙarin girma
Rundunar sojin Najeriya, a ranar Juma’a, ta ce ta kara wa manyan hafsoshi 122 karin girma.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce Birgediya Janar 52 ne suka samu karin girma zuwa mukamin Manjo Janar, yayin da Kanar 70 kuma aka daukaka zuwa matsayin Birgediya Janar.
KARANTA WANNAN LABARIN: DSS ta hana ni magani tsawon kwanaki tara – Nnamdi Kanu ya koka
“Saboda kyakkyawar hidimar da suke yi wa kasa, a ranar Alhamis 15 ga Disamba, 2022 Majalisar Sojoji ta amince da karin girma ga manyan hafsoshi zuwa mukamin Manjo Janar da Birgediya Janar,” in ji shi.
Ya ce Birgediya-Janar AA Ayanuga na Sashe Sauyi da Kirkire-Kirkire EH Akpan na Kwamandan Rundunar Operation HADIN KAI, NM Jega na Hedikwatar Tsaro, JO Ugwuoke na Sashen Dabarun Sojoji, PAO Okoye na Sashen Ayyukan Sojojin, EF. Oyinlola na sashen ayyuka na musamman da shirye-shirye, AA Adekeye na 21 Special Armored Brigade, AE Edet na Nigerian Army School of Electrical and Mechanical Engineers, AB Mohammed na hedkwatar rundunar soji da kuma MT Usman na hedkwatar Guards Brigade na cikin wadanda an kara masu girma zuwa mukamin Manjo Janar.
Wasu daga cikin Kanar din da aka daukaka zuwa mukamin Birgediya Janar sun hada da Kanar AO Ajagbe, JO Ogbobe, MG Hammawa, SS Bello, SOG Aremu, NG Mohammed, OI Odigie, CA Osuagwu, MO Eteng, ED Idima, da dai sauransu.
Shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya bukaci jami’an da aka kara wa karin girma da su kasance masu mai da hankali, rashin son kai da biyayya ga aikin da suke yi wa kasa domin tabbatar da kwarin guiwa da amanar da babban kwamandan rundunar sojin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ɗora masu ds sojojin Najeriya da ma dukkan ‘yan Najeriya..
A wani labarin kuma: 2023: Kiristocin Arewa suna matuƙar Son hadin kan yankin – Shugaban CAN
Yayin da kasar nan ke kara kusanto da zaben 2023, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN a Jihohin Arewa 19 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, Rev Dr Yakubu Pam ya bayyana cewa muradin Kiristocin Arewa shi ne hadin kai da zaman lafiya a yankin.
Ya bayyana hakan ne a shekarar 2022 a yayin taron addu’o’i na kwanaki uku da kungiyar CAN ta shirya a jihohin Arewa da kuma FCT, wanda aka gudanar a Cibiyar Social Center da ke Kaduna.