An Buƙaci Gwamnatoci Da Su Yi Koyi Da Gwamnan Yobe Wajen Magance Matsalar Tsaro
Shugaban Kungiyar Makiyaya ta Kasa da ake kira “Kulen Allah”, Khalil Muhammad Bello, yayi kira ga Gwamnatin Tarayya da wasu Gwamnatocin jihohi da suyi koyi da Gwamnan Jahar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni wajen magance matsalolin tsaro dake addabar yankunan su
Yayi wannan kiran a wata sanarwa da ya fitarwa manema labarai ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, 2024.
KARANTA WANNAN LABARIN: Duk da matsin rayuwa: Gwamnatin Najeriya tace tana asarar N400bn duk wata saboda tallafin mai – Ministan Kudi
A makwannin da suka gabata, an samu matsalolin tsaro a wasu yankunan Jahar Yobe wanda hakan ya janyo hasarar dukiya mai yawa har ma da rayuka.
Tashe-tashen hankulan wadan da suka barke tsakanin manoma da makiyaya a kauyen gurjaje dake Karamar hukumar Fika da kuma wasu sassan Karamar hukumar Fune a Jihar Yoben, sun dauko hanyar yawaita a Jahar.
Sai dai kuma daga aukuwar hakan, Gwamnan Jahar, Mai Mala Buni ya dauki matakan gaggawa wajen dakile su.
Sakamakon haka ne, Shugaban Kungiyar Makiyaya ta Kasa da ake kira “Kulen Allah”, Khalil Muhammad Bello, ya fidda wata takarda ga manema labarai, inda yace akwai bukatar Gwamnatin Tarayya da sauran Gwamnatoci suyi koyi da irin wannan salo.
A cewar Khalil Bello, Gwamna Buni ya kafa kwamitocin Sulhu wadan da suka kunshi manoma da makiyaya, Sarakunan Gargajiya, Jami’an Tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Yace wadannan nan kwamitoci sun taka rawar gani inda a yanzu haka dai al’amura sun soma daidaita.