An tasa keyar wani likita mai suna Kadev Kenneth Kelvin a gidan gyaran hali na gwamnatin tarayya da ke Makurdi kan zargin sa-in-sa ta yanar gizo, kamar yadda Punch ta rawaito.
Wata Kotun Majistare ta Jihar Benuwe da ke zamanta a Makurdi babban birnin Jihar Binuwai ce ta tasa keyar likitan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Ribas Ta Kori Shugaban Hukumar Kula Da Asibitin Jihar
An rawaito wanda ake zargin ya wallafa a shafinsa na Facebook ne a ranar 12 ga watan Maris, 2023 inda ya bayyana cewa ya dinke duburar sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na jihar Benue Bemgba Iortyom a gidan yarin Abuja a shekarar 2017.
Rahoton farko na ‘yan sanda ya ce “A ranar 13/03/2023, kwamishinan ‘yan sandan D.K Iorhemba da Co ya rubuta a matsayin Barista da Lauya a madadin Bemgba Iortyom, Sakataren Yada Labarai na PDP jihar Benue, yana bayyana cewa Kadev Kenneth Kelvin, likita ne wanda ke aiki a Kadev Health Systems Services mai lamaba 9 daura da Holy Covenant dake kan titin Otukpo, Makurdi.
Rahoton ya kara da cewa likitan da aka ambata ya yi kalaman batanci game da Bemgba a ranar 12/03/2023 da misalin karfe 11 na dare yayin da yake tattaunawa da wani Gabriel Terungwa Shange. An ruwaito ya ce, ‘Yayana, idan Bemgba Iortyom na son yin jima’i, ka sanar da ni, ranar da ya gano haka, ni ne likitan da ya dinka masa leda a lokacin da aka yi luwadi a gidan yarin Abuja a shekarar 2017 shi ya tare ni.’
Bayan binciken da suka yi, ‘yan sandan sun ce an kama likitan ne kuma bayanin da aka yi a Facebook hoto ne domin shaida kuma ya amsa laifin da aka ce ya aikata.
A cewar ‘yan sanda, laifin ya ci karo da sashe na 24 (1) (a) (b) (i) na dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo shekarar 2015. Lokacin da karar ta taso, ba a dauki wani kara don neman hurumi ba.
Dan sanda mai shigar da kara, Isfekta S.O Itodo ya sanar da kotun cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. Ya roki kotun da ta kara kwanan wata domin baiwa masu gabatar da kara damar tabbatar da tuhumar da ake musu.
A wani labarin kuma, Zababben Mataimakin Shugaban Kasa Ya Ziyarci Tsoffin Shugabanin Mulkin Soji 2 A Minna
Zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya nemi jagoranci da goyon bayan tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), da tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), don sake gina Najeriya.
Shettima, wanda ya bayyana hakan bayan ganawarsa da tsaffin shugabannin biyu daban-daban a Minna, babban birnin jihar Neja a jiya, ya ce sun kai ziyarar ne domin duba su domin gudanar da azumin watan Ramadan.