Wata kotun majistare da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta bayar da umarnin garkame wasu mutane bakwai da ake zargi da laifin kashe wani dalibi, Ridwan Ajibiye, a rikicin da ya barke a garin Malete.
Wadanda ake zargin dukkansu daliban sun hada da Victor Okpara, Zubair Baba, Samuel Ogundele, Stephen Oluwafemi, Oyebanji Sodiq, Oladipupo Mukaram da kuma Salau Joshua. Suna tsakanin shekaru 22 zuwa 26.
Ana tuhumar su da laifin hada baki, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, zama mambobin kungiyoyin asiri, da kuma kisan kai.
Laifukan sun ci karo da sashe na 6(B) da 27(IXC) na Fashi da Makamai ( tanadi na musamman) Dokar CAP R11 LFN 2006, Sashe na 221 na dokar hukunta manyan laifuka da ake hukuntawa a karkashin sashe na 14 na Dokar Hana asirri da Kungiyoyin asiri na 2016.
Lauyan wadanda ake kara, Barista Toyin Onalolapo, ya bukaci kotun da ta bayar da belinsu.
Mai shari’a O. A. Adeniyi, a hukuncin da ta yanke, ta tasa keyar wadanda ake zargin a gidan gyaran hali, sannan ta dage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Fabrairun 2022 domin ci gaba da tuhumar su.