An daure wani mutum wanda ya samu hotunan al’aurar mata da dama ta hanyar yin karyar cewa shi likita mace ne a kafafen sada zumunta a kasar Singapore,
LIB ta ruwaito.
Kotun Singapore a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba ta gano cewa Ooi Chuen Wei, mai shekaru 37 asali dan Malaysia ne. Kuma ta kama shi dumu-dumu da aikata ha’inci. An yi masa daurin shekaru uku da watanni uku a gidan gyaran hali.
Ooi ya yi amfani da sunan bogi don tuntubar mata da su cikashe takarda wacce ke dauke da tambayoyi akan al’aura da rayuwar tarayyarsu da mazajensu kamar yadda takardar kotu ta bayyana.
Tsawon shekaru hudu, Wei ya yaudari mata 38 kuma ya samu hotunan tsiraicinsu guda 1,000 da bidiyoyinsu. ‘Yan sanda sun gane hakan ne a watan Yulin 2021 yayin da wata mata ta fara zargin Ooni daga nan ta gane cewa babu wani likita haka inda ta kai kara wurin ‘yan sanda.
‘Yan sanda sun je har gidan Ooni inda su ka kwace na’urorinsa. Yayin bincike ne ya bayyana cewa yaudarar mata yake yi kamar yadda takardun kotu su ka nuna.
Mataimakin mai gabatar da kara, R. Arvindren ta bukaci kotu ta daure shi na akalla shekaru uku da watanni takwas ganin yadda ya yaudari mata da dama kuma Ooni zai iya ci gaba da hakan.
Arvindren ya bayyana cewa yana gamsar da sha’awarsa ne ta ganin hotuna da bidiyoyin tsiraicin mata.
‘Yan Sanda Sun Damke Wani Mutum Dauke Da Katunan Zabe Guda 101 A Sokoto
Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta samu nasara cafke wani mutum mai suna Nasiru Idris da ke karamar hukumar Sabon Birni dauke da katin zabe na dindindin guda 101.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, kwamishinan ‘yan sanda, Hussain Gumel, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Sabon Birni a ranar 10 ga watan Oktoba, bayan samun sahihan bayanan sirri.
Ya kara da cewa wanda ake zargin ba zai iya bada bayanin yadda ya samu katin zaben na PVCs ba
“An yi hasashen cewa masu wadannan katunan ba ‘yan karamar hukumar Sabon Birni ne kadai ba, za su iya kasancewa sun fito daga sassan jihar saboda ba mu iya gano wadanda suka mallaki katinan PVC din ba,” inji shi.
Sai dai ya yi kira ga jama’a musamman wadanda katinan su ya bace da su zo hedikwatar hukumar su duba.
CP ya ce ‘yan sanda za su mayar da duk katinan da ba a karba ba zuwa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) bayan wata daya.
A halin da ake ciki, rundunar ta kuma yi wa sabbin jami’ai shida da aka kara wa girma ado.