An fara wata ganawa tsakanin babban hafsan sojojin Habasha da kwamandan ‘yan tawayen Tigray People Liberation Front (TPLF) a Nairobi babban birnin kasar Kenya.
BBC ta ruwaito cewa, Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan batun kwance damarar dakarun ‘yan tawayen bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu a birnin Pretoria na Afirka ta Kudu a makon jiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kungiyar Neja Delta Ta Bukaci Buhari Ya Tsige Ministar Jin Ƙai Sadiya Farouq
An fara tattaunawar ne a ranar Litinin karkashin jagorancin wakilin kungiyar Tarayyar Afirka, kuma tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, da tsohon shugaban Kenya Uhuru Kenyatta.
Taron wanda aka shirya na tsawon kwanaki uku, zai tattauna hanyoyin kwance damarar dakarun ‘yan tawaye tare da samar da taswirar isar da kayayyakin agaji da maido da ayyuka a yankin na Tigray.
A bisa yarjejeniyar zaman lafiya, ya kamata a kammala kwance damarar yaki makwanni biyu bayan taron manyan kwamandojin.
Rikicin da aka kwashe shekaru biyu ana yi ya janyo asarar rayuka da dama tare da raba miliyoyi mutane da muhallansu.
A WANI LABARIN KUMA: Ekweremadu Zai Yi Bikin Kirsimeti Da Sabuwar Shekara a Gidan Yari
Kotun manyan laifuka da ke birnin Landan na kasar Birtaniya ta dage shari’ar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu.
Yayin zaman shari’ar an dage karar daga watan Mayun 2023 zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2023