….Kasashen Saudiyya, Qatar, Turkiyya da hadaddiyar Daular Larabawa sun sanar da gobe a matsayin ranar Idin karamar Sallah 1 ga watan shawwal.
An ga jinjirin watan Shawwal a kasar Saudiyya a yau Alhamis 20 ga watan Afrilu.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Hakan na nufin Idin Al-Fitr zai kasance ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu.
KARANTA HAKANAN Sarkin Musulmi Ya Sanar Da Ganin Watan Azumin Ramadanu
Kazalika Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa sun sanar da cewa za a gudanar da Sallar Idi a ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu bayan ganin jinjirin wata.
Don haka ranar alhamis ita ce ta karshe kuma 29 ga watan ramadan shekara ta 1444 bayan hijira.
An ga jinjirin watan Shawwal ne ta hanyar amfani da fasahar daukar hoto. An lura da shi a fadin Masarautar a duk wuraren lura da suka hada da Sudair da Tumair.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Kotun kolin Saudiyya ta tabbatar da ganin wannan lamari, ta kuma sanar da ranar Juma’a a matsayin ranar Idi.
A Wani Labarin Kuma ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 17 Da Ake Zargin Masu Satar Mutane Ne, Sun Ceto Mutane 5
Rundunar ‘yan sanda a jihar Nasarawa ta kama wasu mutane 17 da ake zargi da yin garkuwa da mutane tare da ceto mutane biyar da suka sace ba tare da an samu rauni ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan yayin da yake holan wadanda ake zargin a madadin kwamishinan ‘yan sandan, Baba Maiyaki, ranar Alhamis din nan a Lafiya.