A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu ma’aikatan gwamnati uku suka gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Birnin Kebbi bisa zarginsu da cin zarafin babban alkalin kotun majistire mai lamba biyu, Umar Salihu-Kokani. Kamar yadda NAN ta ruwaito.
Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Aliyu Shehu, Yahyah Badare, Surajo Shehu dukkan ma’aikatan ma’aikatar ilimi ta jihar Kebbi da laifin hada baki, karya, cin zarafi da batanci ga Alkalin wanda ta ce, hakan ya sabawa sashe na 373 na dokar Penal code na jihar Kebbi na shekarar 2021.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kamfanin Jiragen Saman Kenya Zai Kori Matuka Jirgin Da Suka Shiga Yajin Aiki
Shiri’ar dai ammata alama da BK/358c’/2022.
Lauyan masu shigar da kara, Malam Jibril Abba, ya shaida wa kotun cewa mutanen uku sun yi wa babban Alkali Kokani hari ne a lokacin da yake alwala a wata masallacin.
Ya ce ‘yan sanda sun kama su ne bayan mai shigar da kara ya kai rahoton lamarin.
Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa ‘yan sanda a shirye suke su fara bayyana hujjoji amma saboda rashin halartar babban shaida zai nemi a dage shari’a.
Sai dai Babu wani lauya da ya wakilce ma’aikatan da ake zargi a gaban kotu.
Alkalin kotun Hassan Kwaido, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba domin ci gaba da bayyana shaidun.
Da yake zantawa da manema labarai bayan dage shari’ar, Lauyan mai kara Sani Dan-Yaro, wanda kungiyar Alhakku human right and social justice organization karkashin Daraktanta na kasa SAEED BIN USIMAN ta dauka, ya bayyana cewa, abun da wanda yake karewa kawai yake bukata shine adalci.
Dan-Yaro ya ce matakin da ma’aikatan gwamnati suka dauka na iya aika wa jama’a wata alama da ba ta dace ba cewa za a iya cin zarafi ko kuma a kai wa wani babban jami’i hari ba tare da wani sakamako ba.
“Abin da muke so shine adalci. Ba ma son yanayin da mutane za su dauki doka a hannunsu kuma su yi imani cewa babu abin da zai faru, “in ji shi.
A WANI LABARIN KUMA: Ku Kuji Amfani Da Muggan Makamai Yayin Yakin Neman Zabe— Rundunar Yan sanda Ga Yan siyasa
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe Ishola Babaita, ya yi gargadi kan amfani da bindigu da sauran muggan makamai a wuraren yakin neman zabe. Kamar yadda Punch ta ruwaito.
Babaita ya kuma gargadi ‘yan siyasa kan amfani da wasu abubuwan tsaro da ba a amince da su a jihar ba, yana mai jaddada cewa wasu ayyukansu na iya haifar da tashin hankali