Tsohon firaministan Malaysia Muhyiddin Yassin a ranar Juma’a ya gurfana gaban kotu bisa tuhumarsa da laifin yin amfani da karfin ikonsa na karbar cin hanci da kuma karkatar da kudade da ke da nasaba da zargin yin amfani da asusun farfado da tattalin arzikin kasar na COVID-19.
Muhyiddin ya kasance Firaminista na tsawon watanni 17 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021, a daidai lokacin da Malaysia ke yakar cutar corona, kuma yanzu yana jagorantar kawancen adawa da gwamnatin Firaminista Anwar Ibrahim. shugaba Najib Razak, wanda a halin yanzu yake zaman gidan yari na shekaru 12 saboda rawar da ya taka a badakalar kudi a asusun saka hannun jari na jihar 1MDB.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abin Takaici – Ronaldo Ya Mayar Da Martani Yayin Da Al-Nasar Ta Sha Kashi A Hannun Al-Ittihad
Muhyiddin mai shekaru 75, an tuhume shi da tuhume-tuhume guda hudu da laifin yin amfani da mukaminsa wajen karbar cin hanci da ya kai adadin ringgit miliyan 232.5 dai dai da (dala miliyan 51.4) ga jam’iyyarsa ta siyasa Bersatu.
Zargin cin hancin ya fito ne daga kamfanonin da aka ba da fifiko ga ayyukan da asusun Covid-19 ke bayarwa.
Kowane tuhume-tuhumen yana ɗaukar daurin shekaru 20 a gidan yari idan aka same da laifin.
Ana kuma tuhumar Muhyiddin da tuhume-tuhume biyu na karkatar da kudade da suka hada da ringgit miliyan 195 da aka saka a asusun Bersatu, a cewar takardar tuhumar.
Kowanne daga cikin wadannan tuhume-tuhumen na iya kaiwa shekaru 15 a gidan yari.
Masu gabatar da kara sun ce a ranar Litinin ne ake sa ran za a gurfanar da shi a gaban kotu na uku na karkatar da kudade.
A zaman kotun na ranar Juma’a, Muhyiddin ya ki amsa duk wasu tuhume-tuhume da ake yi masa, sannan ya bukaci a yi masa shari’a.
An bayar da belinsa amma an umarce shi da ya mika fasfo dinsa.
– ‘Adalci a kotu’ –
A cikin wata sanarwa da ya fitar, tsohon firaministan ya dage cewa “babu ko daya na kudin jama’a da ya shiga aljihuna a lokacin da nake rike da mukamin firaminista”.
Zargin ya zo ne kwana guda bayan da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Malaysia (MACC) ta yi wa Muhyiddin tambayoyi, kuma daga bisani ta kama shi.
Ya musanta aikata wani laifi kuma ya zargi kawancen da ke mulki Anwar da tursasa siyasa don bata masa suna da jam’iyyarsa gabanin zaben jihohi a watan Yuli.
“Ni da tawaga ta lauyoyi za mu yi aiki tukuru don ganin an yi mana adalci a kotu,” in ji shi, yana mai kira ga magoya bayansa da kada su yi zanga-zangar kan tituna.
Anwar dai ya musanta yin katsalandan a harkokin shari’a.
MACC ta kaddamar da bincike kan zargin karkatar da kudaden annobar COVID-19 da Bersatu ta yi tare da daskarar da asusun bankin jam’iyyar a watan jiya.
An kuma tuhumi shugabannin Bersatu biyu da laifin cin hanci da rashawa da suka shafi shirin kara kuzari.
Muhyiddin dai ya yi fice ne a zamanin tsohon firaminista Najib, wanda har yanzu yake fuskantar tuhume-tuhume da dama na cin hanci da rashawa.
Ya yi karo da Najib ne a shekarar 2015, lokacin da aka kore shi daga aiki bayan ya soki gwamnati kan badakalar 1MDB.
Daga baya Muhyiddin ya shiga jam’iyyar da tsohon firimiya Mahathir Mohamad ya kafa inda ya taimaka wajen kawar da Najib da jam’iyyarsa ta United Malays National Organization (UMNO).
Sa’an nan, a cikin yanayin siyasar Malaysia, ya sake haɗa hannu da UMNO don samun isasshen goyon baya don zama Firaminista.
A wani labarin kuma, Ko Kaɗan Ban Damu Don PDP Ta Haɗa Kai Da Sauran Jam’iyyu – Uba Sani
Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya da kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Uba Sani, ya ce bai damu da jam’iyyun siyasar da suka amince da dan takarar babban abokin hamayyarsa Isah Ashiru Kudan na jam’iyyar PDP ba.
Sani ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Arise TV game da yiwuwar jam’iyyarsa ta lashe kujerar gwamna a jihar.