By Abbas Yakubu Yaura
Wani matashi dan shekara 21, Stephen Monday, ya gurfana a gaban wata kotun majistare dake Ebute Meta, jihar Legas, bisa zargin cin zarafi da kuma yin sata.
Wanda ake zargin ya ci zarafin wani jami’in dan sanda, Insifekta Folorunsho Lawal, yayin da dan sandan yake gudanar da aikinsa a unguwar Otto, Ebute Metta.
An kuma tuhumi wanda ake zargin da yaga kakin Lawal ranar Litinin a cikin tuhume-tuhume uku da suka shafi kai hari, sata da kuma halin da ka iya haifar da rashin zaman lafiya.
Laifin tuhumar ya kara da cewa, “Kai, Stephen Monday, da sauran jama’a a yanzu haka, a ranar 29 ga watan Janairu, 2022, da misalin karfe 03:30 na rana, a G-Express, Otto, Ebute Metta, a gundumar Majistare ta Legas, ka ci zarafin wani Insifeto Folorunsho Lawal yayin da yake gudanar da aikinsa na shari’a ta hanyar lakada masa duka tare da yaga kakin sa, inda ka aikata laifin da zai hukunta ka a karkashin sashe na 173 na dokar laifuka ta jihar Legas shekarar 2015.
“Cewa, Stephen Monday, da sauran jama’a, a rana daya, lokaci da wuri, a karamar hukumar da aka ambata, kun gudanar da ayyukan ku ta hanyar da za ta haifar da rashin zaman lafiya ta hanyar kai wa Sufeto Lawal hari a lokacin da yake gudanar da aikinsa na doka, don haka ka aikata laifin da za a hukunta ka a karkashin sashe na 168 (d) na dokar aikata laifuka ta Jihar Legas shekarar 2015.
“Cewa, kai Stephen Monday da sauran jama’a a rana daya, lokaci da wuri a karamar hukumar da aka ambata a baya, kun sace naira 80,000 da wata Hula da aka kiyasta kudinta ya kai N20,000, mallakin wani sufeto Lawal, wanda hakan ya sa kuka aikata wani laifi, hukuncin a karkashin sashe na 287 na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.”
Alkalin kotun, Misis F. F. George, ta bayar da belin wanda ake kara sannan ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 7 ga watan Fabrairun 2022 domin yi masa shari’a.