By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta cafke wata mata mai suna Omoyemi Opeyemi bisa zargin ta da raunata wani yaro mai suna Joel Sunday kan zargin satar nama a cikin tukunyar miya.
A cikin wani faifan bidiyo an ga yaron dan shekara tara yana kuka da alamu a jikinsa wanda ke nuni da cewa an yanki jikinsa da reza yayin da jini ya zuba da yawa a jikinsa.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a unguwar Adebowale dake Akure, babban birnin jihar Ondo.
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce wanda ake zargin “za a sanya ta, ta fuskanci fushin doka”.
PPRO ta ce ‘yan sanda sun gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu ranar Litinin yayin da ake ci gaba da shari’ar a kotun majistare da ke kan titin Ondo, Akure.