An hana ‘yan jarida da ke neman ziyartar wurin da ginin bene mai hawa bakwai ya ruguje a tsibirin Banana na jihar Legas,Punch ta rawaito.
An bukaci manema labarai daga gidajen jaridu daban-daban da suka hada da The PUNCH, Channels TV, TVC, Arise, Guardian da sauran su da su tsaya a wajen kofar shiga gidan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Shugaban Kasa: Dalilan Da Suka Sanya Na Doke Ku – Martanin Tinubu Ga Obi
Galibin ‘yan jaridan sun shaida wa wakilinmu cewa sun shafe sama da sa’o’i biyu a wajen suna jira.
Da yake mayar da martani kan dalilin da ya sa hukumar ta dauki matakin, hukumar ta ce, “Ba sa son ’yan daba su shiga cikin gidan domin dakile tabarbarewar doka da oda.
Hukumar, duk da haka, ta samar da tanti ga ‘yan jarida masu jiran Neman labarai.
Tsibirin banana na daya daga cikin unguwanni mafi tsadar rayuwa a Najeriya, inda wasu masu hannu da shuni ke da arziki a kasar. Ba za a iya samun damar zuwa wurin ba tare da samun lambar shiga daga mazaunan ba.
A wani labarin kuma,Zaben Gwamnan Kogi: Kotu Ta Soke Jerin Sunayen Wakilan APC, Ta Bada Umarnin Sake Sabon Taro
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja a jiya ta soke taron mazabu da na kananan hukumomi na jam’iyyar APC da ta gudanar da nufin tsayar da dan takararta a zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Kotun a cikin hukuncin da mai shari’a James Omotosho, ya yanke, ta ce taron da aka gudanar a ranar 7 ga watan Fabrairu, ba a gudanar da shi bisa tanadin dokar zabe ta 2022 da kuma kundin tsarin mulkin APC ba.