By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni daga babban birnin Guinea-Bissau, sun bayyana cewa an ji karar harbe-harben bindiga a kusa da fadar shugaban kasar.
Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce sojoji sun kewaye ginin fadar shugaban kasar.
Kazalika rahotanni sun tabbatar da cewa Shugaba Umaro Sissoco Embaló yana cikin fadar lokacin da ake harbe-harben.
Lamarin na faruwa ne a yayin da Shugaba Embaló da Firaminista Nuno Gomes Nabiam suke gudanar da taro.
Wani mazaunin birnin ya shaida wa manema labarai cewa an kashe wani dan sanda a sakamakon harbe-harbe.
Mutumin ya kara da cewa wasu mutane cikin farin-kaya dauke da makamai sun bude wuta a wurin da shugaban kasar da firaministan suke yin taro.
Wasu majoyoyi sun ce ba a san inda shugabannin suke ba a halin yanzu