An bayyana Iyaye Mata a Yankin karamar hukumar Gabasawa da cewa sune kashin Bayan tarbiyar Al-umma.
Me Dakin Gwamnan Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ce ta bayyana Hakan lokacin Kaddamar Da Jakadun Yaki Da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi Mata su Goma Sha Daya na yankin.
Farfesa Hafsat Ganduje dai ta samu wakilcin wakilcin Mai Bawa Gwamnan Kano Shawara Akan Kungiyoyi Masu zaman Kansu Kuma Ma’ajin Jam’iyar APC ta Jaha Hajia Yardada Maikano Bichi.
Da take Jawabi tun da fari, Shugaban Kwamitin, Kuma me Bawa Gwamna Shawara Akan Harkar Lafiya Dr Fauziyya Buba Idris wadda Sakatariyar Kwamitin Hajia Amina Haruna Shanono tayi jawabi a madadinta, ta roki Matan yankin da su yi Aiki tukuru da Jakadun Yaki Da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi na karamar hukumar Dan Ganin an samu Nasarar da Ake nema.
Anata Jawabi Mataimakiyar Kwamandan Hisba bangaren Mata malama ummalkhulsum Kasim ta yi bayani Mai tsawo game da Mahangar Addini Akan Ta Ammali Da Miyagun Kwayoyi, inda ta Jawo Ayoyin Alqur’ani Maigirma tare da Hadisan Annabi S. A. W da sukai Hani da ta’ammali da Miyagun Kwayoyi.
Sauran wadanda sukai Jawabai a yayin taron sun hada da Shugabar Mata ta Jam’iyar APC ta Jiha Sayyada Fatima Abdullahi Dala, da Mai Dakin Shugaban Karamar Hukumar Gabasawa Hajia Rafiatu Mahe Garba Garun Danga.
An Dai gudanar da taron ne a Cibiyar Yada Addinin Musulunci dake Zakirai, inda ya Sami Halarta Shugaban Karamar Hukumar Gabasawa Alhaji Mahe Garba Garun Danga, da Matan Zababbun Kansilolin Na Mazabu Goma Sha Daya na yankin.