Wani malamin makarantar sakandare a jihar Ogun, Lateef Olaniran, ya shiga hannun jami’an tsaro bisa zargin yi wa wata budurwa fyade da aka sakaya sunanta.
Olaniran, wanda aka ce dan asalin karamar hukumar Ipokia ne a jihar Ogun, malamin lissafi ne a makarantar Ebenezer Grammar School, Iberekodo, Abeokuta.
Karanta nanGwamnan Osun Ya Karyata Batun Kashe Miliyan 400 Duk Wata
Ma’aikaci ne a Hukumar Kula da Koyarwa ta Jihar Ogun mai lamba, OGNO.30650.
Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Adijat Olaleye ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.
A cewarta, an kama Olaniran ne a ranar Asabar, a lokacin da wata ‘yar tawagarta ta samu waya daga wata budurwa, inda ta ce wani mutum ya yi mata fyade.
Kwamishiniyar ta ce ma’aikatar ta dauki matakin ne inda ta gano wadda abin ya faru da ita wadda ta ce an kai ta dakin gwaje-gwaje domin yi mata gwaje-gwaje daban-daban kafin daga bisani aka kai ta ofishin ‘yan sanda don bayar da rahoto.
Daga baya mun tafi tare da ‘yan sanda zuwa gidan wanda ake tuhuma amma bayan kwankwasa da yawa, ya ki bude kofar mun sami ɗan’uwa ga mai gidan da ya taimaka mana mu shiga harabar gidan ta bayyana.
Adeleye ya bayyana cewa a lokacin da suka shiga harabar wanda ake zargin, mun ji kukan yarinya na neman agaji, kuma tare da goyon bayan ’yan sanda, mun kama Mista Olaniran Lateef Adewale wani malamin lissafi na makarantar sakandare a Ebenezer Grammar School Iberekodo, Abeokuta.
A wani labarin kumaBoka Ya Harbe Wani Mutum Har Lahira Yayin Gwajin Maganin Bindiga A Bauchi
Kwamishinar ta kara da cewa yarinyar tana kuka a dakin malamin a lokacin da aka kama shi ta kuma zarge shi da yin lalata da ita da kuma yi mata barazanar kashe ta idan ba ta nemi danginta su aika masa kudi ba.
Adeleye ta tabbatar da cewa an tasa keyar wanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sandan jihar Ogun domin gudanar da bincike.