An kama masu damfarar intanet 36 a Kaduna
Wadanda ake zargin sun hada da maza 35 da mace daya, an kama su ne a Sabo Kaduna da Narayi Highcoast da Layin Dogon Iche Samaru a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.
Kamasu ya biyo bayan sahihan bayanai kan zargin da ake yi musu na aikata laifukan da suka shafi intanet.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin magance digirin bogi
Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayoyi 43 da kwamfutoci biyar.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kara da cewa za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.
A wani labarin kuma:Duk da matsin rayuwa: Gwamnatin Najeriya tace tana asarar N400bn duk wata saboda tallafin mai – Ministan Kudi
Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya ce tallafin man fetur na janyowa Gwamnatin Tarayya asarar Naira biliyan 400 duk wata.
Edun ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan Talabijin na Channels wanda DAILY POST ta sa ido.