Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka kware wajen yin garkuwa da mata a garin Makurdi da kewaye.
An yi holan wadanda ake zargin a gaban ‘yan jarida yayin da aka ruguje ginin da suke amfani da shi wajen ajiye wadanda abin ya shafa.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/kasar-jamus-ta-dakatar-da-ayyukan-sojinta-a-mali/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro, Laftanar Kanal Paul Hemba (mai ritaya) ya ce an samu mutanen biyu da karbar makudan kudin fansa daga iyalan wadanda abin ya shafa.
Ya ce an ci karo da su a wani samame na karshe da ‘yan sanda suka yi, inda ya ce rushe kadarori da aka yi amfani da su wajen yin garkuwa da mutane ya yi daidai da dokar jihar Binuwai kan al’amuran da suka shafi al’ada, garkuwa da mutane ta (2017).
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Wale Abass, wanda ya gabatar da wadanda ake zargin, ya bayyana cewa an dauke su ne daga maboyar su da ke kan hanyar Gboko a cikin garin Makurdi a ranar 9 ga watan Agusta.
Abass ya ce wadanda ake zargin a lokacin da suke tserewa daga wurin a wani samame da suka kai na karshe ba tare da nasara ba, sun jefar da waya wanda hakan ya baiwa ‘yan sanda damar kama su.
Ya kara da cewa wadanda ake zargin ‘yan tawagar mutane hudu ne, yana mai jaddada cewa a halin yanzu jagoransu da wani mutum sun tsere.
Wadanda ake zargin; Solomon mai shekaru 25 da Achoho mai shekaru 30 a lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida sun amince da aikata laifin.
DAILY TRUST