- An kama wani dan kasar Uganda da aka nada a matsayin alkali a watan Yunin 2023 yana rubuta jarabawar shari’a ga budurwarsa.
- An kama mutumin mai suna Semwogerere Ammaari tare da mika shi ga ‘yan sanda domin fuskantar tuhuma
- Sai dai abin takaicin shi ne, Semwogerere an kama shi da aikata wannan aika-aika, kuma a yanzu hukumar shari’a ta Uganda ta sauke shi daga mukaminsa.
An kama wani mutum a kasar Uganda bisa laifin zana jarabawa ga budurwarsa.
Mutumin mai suna Semwogerere Ammaari, wanda aka fi sani da Mukisa Anthony, an kama shi ne a cibiyar bunkasa shari’a, LCD, Uganda, kamar yadda majiyarmu ta ruwaito.
Semwogerere, wanda aka naɗa a matsayin alkalin kotu a watan Yunin 2023, ya je zana jarabawar shari’a a madadin budurwarsa, Irene Mutonyi.
KARANTA WANNAN LABARIN:
Wata Ba Amurkiya Ta Biya Kuɗin Kitso Naira Dubu 68 A Afirka Ta Kudu
Da yake tsokaci game da ci gaban, darektan LDC Frank Nigel Othembi ya ce:
“Mun kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda kuma ana tuhumarsa da laifuka biyu da suka haɗa da furta wata takarda ta karya da ta saɓa wa sashi na 351 na kundin laifuffuka da kuma aikata laifin da ya saɓa wa sashi na 381 na kundin laifuffuka, inda aka tura shi gidan gyaran hali har zuwa uku ga wannan watan na Agusta, 3. 2023.
Za mu tabbatar da cewa an gurfanar da wannan me shari’ar gaba ɗaya har zuwa ƙarshe, gami da duk sauran masu laifi.“
A halin yanzu LDC tana gudanar da jarrabawar karshe ta a duk cibiyoyinta guda uku dake a Kampala, Lira da kuma Mbarara.
LDC ba ta yarda da duk wani rashin ɗa’ar jarrabawa ba. Za kuma a ci gaba da aiwatar da manufofin mu na rashin haƙuri ga kowane irin wannan hali.”
A wani sakon da ta wallafa a shafin Twitter, hukumar kula da shari’a ta Uganda ta ce za a soke naɗin mutumin da aka kama kamar yadda wani ɓangare na sanarwar ya karanta: “Hukumar kula da harkokin shari’a ta naɗa Ssemwogerere Ammaari Musa a matsayin jami’in shari’a a ranar 12 ga watan Yunin 2023 tare da wasu mutane 86 zuwa matsayin majistare mai mataki na daya a shari’a. Mista Semwogerere ba zai cigaba da aiki a ma’aikatar shari’a ba.”