Wani matashi dan shekara 24 mai suna Yusuf Bello mazaunin jihar Legas ya amsa laifin satar nadin wayar lantarki 15.
An gurfanar da Bello a gaban Alkalin Kotun, Mista L K. Layeni, bisa zargin sata, kuma ba tare da bata lokacin Shari’a ba ya amsa laifinsa.
Bayan rokon da ya yi, kotun ta bayar da umarnin a tsare shi a ofishin ‘yan sanda na Ajangbadi, har sai an yi nazari a kan gaskiyar lamarin da kuma yanke masa hukunci.
Dan sanda mai shigar da kara, Dokta Simon Uche, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Mayu a unguwar Iya Juwon da ke Ajangbadi a Ojo, jihar Legas.
Ya ce wanda ake tuhumar ya sace bandir din wayar 15 masu girma dabam na wani mutum mai suna Ifeanyi Ndibe wanda Mista Ibrahim Sulaimon ya wakilta.
Uche ya ce wanda ake tuhumar ya saci nadi guda tara na wayar lantarki mai nauyin 2.5mm wanda kudinsa ya kai N155,000, zuwa N250,000.
Jimillar kudaden abinda ya sace sun kai N266, 850,” kamar yadda ya shaida wa kotun.
Laifin da ake zargin ya sabawa tanadin sashe na 287 na dokar laifuka ta jihar Legas, na shekarar 2015.
Kotun ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 22 ga watan Yuni domin duba gaskiya tare da yanke hukunci kan wanda ake kara.