Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a ranar Talata ta tabbatar da cafke wasu mata biyu da ake zargi da hannu a bacewar jaririya a sashin binciken manyan laifuka na jihar, da ke Yaba.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce har yanzu ba a gano jaririn ba.
Jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa wani dan sanda da ke aiki da sashin SCID, Samuel Ukpabio, ya dauki yaron daga hannun mahaifiyarsa, Fortune Obafuoso, a lokacin da yake ikirarin cewa yana rike da mukamin ma’aikatar gwamnati.
KU KARANTA KUMA Asibitin AKTH Ya Magantu Kan Salwantar Da Hannun Wani Jariri A Kano
Obafuoso ya ce a ranar Juma’a, 23 ga watan Disambar 2022, lokacin da ta haihu, dan sandan ya kama ta tare da ‘ya’yanta, ciki har da sabuwar haihuwa, wajen SCID bisa zarginta da sayar da jaririn, zargin da ta ƙaryata.
Matashiyar mai shekaru 35 ta bayyana cewa Ukpabio, a yayin da yake yi mata tambayoyi a wurin ’yan sanda, da karfi ya dauki jaririn tare da mika shi ga wata mata da har yanzu ba a ganta ba.
Daga baya dan sandan ya ba ta Naira 15,000, kuma ya yi mata barazanar cewa ba za ta dawo da jaririn ba.
Ya sake aika mata da Naira 170,000 bayan ta ci gaba da neman yaron.
Kakakin ‘yan sandan, Hundeyin, ya tabbatar da kama dan sandan.
Da yake bayar da karin haske kan lamarin a ranar Talata, ya ce, “An kama wasu mata biyu; Insifeto (Ukpabio) ya ambaci wanda ya ba wa jaririn, muka kama shi. Mutumin yana tsare a yanzu. Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wannan mutumin ya ambata cewa ta ba wa wani mutum jaririn kuma an kama mutumin an tsare shi.
“Dukansu ba su musanta karbar jaririn ba amma har yanzu ba mu san inda jaririn yake ba. Har yanzu muna aiki kuma zuwa karshen gobe (Laraba), ya kamata mu iya bayyana inda suka kai jaririn. Don haka, a halin yanzu muna da mutane uku a tsare; sifeto, da matan biyu.”
A halin da ake ciki, Daraktan kungiyar Amnesty International a Najeriya, Osai Ojigho, ya ce yadda ‘yan sanda suka yi wa Obafuoso abu ne mai ban tsoro, inda ya ce dole ne a yi adalci kuma jaririn ya dawo.
A Wani Labarin Kuma Likitocin NARD Suna Barazanar Shiga Yajin Aiki A Fadin Kasar Nan
Kungiyar likitocin Najeriya NARD ta yi barazanar shiga yajin aikin gama gari idan gwamnatin tarayya ta ki biya mata bukatunta.
Kungiyar a cikin wata wasika da ta aikewa Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire, mai dauke da sa hannun shugabanta, Dokta Emeka Innocent Orji, ta ce za a fara gudanar da yajin aikin ne idan ba a magance matsalolin ba a gaban majalisar zartarwa ta kasa ta Janairu 2023 (NEC) taron da aka shirya gudanarwa tsakanin 24 zuwa 28 ga Janairu.