Jami’an ‘yan sandan jihar Adamawa sun kama wasu mutane hudu bisa zargin su da ragewa shanu da tumakin mutane hanya.
Ana zargin mutanen hudu sun sace shanu 73 da tumaki 346.
KARANTA WANNAN: Gwamnonin PDP Zasu Gana Domin Tattauna Halin Da Jam’iyyar Ke Ciki
A cewar rundunar, jami’an ‘yan sanda da ke hedikwatar ‘yan sanda reshen Gombi ne suka yi kamen wadanda suka aikata satar tare da mafarautan yankin yayin gudanar da bincike mai zurfi a kauyen Amtasa da ke tsakiyar karamar hukumar Hong ta Adamawa.
Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Suleiman Nguroje, tace “wadanda ake zargin a lokacin da ake yi musu tambayoyi sun amsa laifin satar shanu da garkuwa da mutane.
Ya kara da cewa “musamman a yankunan kauyukan Zumo/Maigero da ke yankin Song, wani yanki na karamar hukumar Gombi, da Maiha, da kuma Jamhuriyar Kamaru.”
An bayyana wadanda ake zargin a cikin sanarwar da suka hada da Dahiru Bashir, dan shekara 22, mazaunin kauyen Kesure dake karamar hukumar Song.
Sannan akwai Tukur Salisu, mai shekaru 19, na Filindi, shi ma a karamar hukumar Song; Muhammed Bello, 21, dake Sigire, Song; da Babangida Ibrahim mai shekaru 18, shima dake Sigire, Song.
A cewar ‘yan sandan, an kama mutanen hudu ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta kai shanun satar ga mutanen da suka tuntuba don karbarsu.
A cewar sanarwar ‘yan sandan, an samu wadanda ake zargin da bindigogi kirar AK-47 guda biyu, shanu 73, da tumaki 346.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, “CP ya kuma ba da umarnin a binciki lamarin cikin hikima kuma a gurfanar da duk wadanda ke da hannu a gaban kotu.”
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Dira Abuja Daga Guinea-Bissau
A yammacin yau Litinin ne shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai birnin Bissau na kasar Guinea-Bissau, domin halartar taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 63. .
Shugaban kasa Tinubu ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 6:30 na yamma a cikin jirgin NAF 001 Boeing 737 Wing na shugaban kasa.