Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ribas, Mustapha Dandaura, ya tabbatar da cewa lamarin kashe mata a Otel a birnin Fatakwal jihar Ribas abin takaici ne. Inda ya tabbatar da cewa; mata kimanin tara ne aka hallaka su ta hanyar shake su a Otel-Otel a jihar ta Ribas a cikin watanni biyu da su ka gabata, kuma rundunarsa ta yi nasarar kama daya daga cikin wadanda suke aikata wannan lafi.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa sun dauki kwararan matakai a yankin Ogoni da ake kashe-kashen, kuma a yau ma har sun kama makamai a wani aiki da suka gudanar na hadin gwiwa tare da sauran jami’an tsaro.