By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane hudu a yankin Obayantor da ke karamar hukumar Ikpoba Okha ta jihar Edo bayan wani rikici da ya barke tsakanin wasu matasa da jami’an sojojin Najeriya.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata a cikin al’ummar yankin da aka ce suna rigingimun shugabanci bayan tsige shugabansu na matasa (Okhaegele) tare da nada wani sabo.
DUBA WANNAN LABARIN: Karamar Hukumar Ungogo Ta Raba Filaye 18 Ga Masu Fama Da Cutar Kuturta Kyauta
Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya yi zargin cewa wani ne ya dauki hayar sojoji ga al’umma da nufin kwato Okhaegele, kuma a lokacin rikicin an kashe sojoji biyu. Ya ce daga baya sojojin suka kaddamar da harin ramuwar gayya ga al’umma.
Wata majiya daga cikin al’ummar yankin ta ce sojojin sun zo da yawa inda suka rika harbe-harbe akai-akai, lamarin da ya tilastawa mutanen yin tururuwa domin tsira da rayukansu. Ya ce an harbe mutane hudu har lahira.
Sai dai mai magana da yawun hedkwatar brigade 4 na rundunar sojin Najeriya dake Benin, Yemi Sokoya, ya musanta cewa an dauki hayar sojoji ga al’umma.
Sannan ya kuma yi watsi da kashe sojoji biyu.
“Ba a dauki sojoji aiki a cikin al’umma ba kuma ba a kashe wani soja ba. Ba harin ramuwar gayya ba ne, amma an yi shi ne bisa bayanan sirri na tara makamai,” inji shi.
Ya ce sojojin sun kwato bindigogin famfo na Ingilishi guda uku, bindiga kirar AK 47 guda biyu, bindigar ganga guda daya, harsashi 32 masu rai, da wayoyi.