Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutane biyar yayin da wasu biyu suka jikkata a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyen Sayaya da ke karamar hukumar Matazu a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO) ASP Abubakar Aliyu ya rabawa manema labarai ranar Talata a Katsina.
Karanta nanKu Daina Yarda Ana Ce Muku Manyan Gobe-Obasanjo Ga Matasa
Ya ce a ranar 6 ga watan Nuwamba, 2023, da misalin karfe 12:55, wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai irin su AK-47 da kuma harbe-harbe a kai a kai, sun kai farmaki kauyen Sayaya da ke karamar hukumar Matazu a jihar Katsina.
Bayan samun rahoton, nan take aka tattara jami’an tsaro zuwa wurin, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar tare da yin nasarar dakile harin.
Duk da haka, an harbe mutane biyar kuma wasu biyu sun jikkata.
PPRO ya kara da cewa maharan sun yi garkuwa da wasu mutane biyar a yayin da lamarin ya faru.
Ya bayyana cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
A wani labarin kumaZa’a Bude Shafin Yanar Gizo Domin Rajistar Aure A Nijeriya-Tinubu
Aliyu ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Mista Aliyu Abubakar-Musa, ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa.
PPRO ya kara da cewa CP ya bukaci jama’a da bayanan da zasu taimaka wajen binciken da su fito su taimaka.
Ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin ganin an kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da samun wata matsala ba tare da damke wadanda suka aikata wannan danyen aikin.