Wasu ‘yan gudun hijira biyu sun mutu sannan sama da gidaje 1000 sun kone kurmus a wata gobara da ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke Maiduguri.
Gobarar ta tashi ne da misalin karfe shida na safe kuma ta dauki sama da awa daya kafin jami’an kashe gobara su shawo kan ta.
Karanta nanBayan Rufewa Ta Wucin Gadi, An Sake Buɗe Sararin Samaniyar Filin Jirgin Saman Fatakwal
Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, Dokta Barkindo Muhammad ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Maiduguri, inda ya ce ‘yan gudun hijira, rundunar hadin gwiwa ta farar hula, jami’an tsaro da wasu nagartattun Samariya sun taimaka wajen kashe gobarar.
Muhammad ya ce hukumar ta fara tantance irin barnar da aka yi a yayin da take kokarin bayar da tallafin jin kai ga wadanda abin ya shafa.
Nan da nan muna samar da buhunan shinkafa 500, barguna da sauran abubuwan da ba na abinci ba domin rage musu radadin wahala,” in ji jami’in. (NAN).
A wani labarin Kuma
Kotu Ba Ta Aiko Mana Umarnin Dakatar Da Yajin Aiki Ba-Kungiyar Kwadago
Kungiyar Kwadago ta Najeriya da kungiyar ‘yan kasuwa sun musanta samun umarnin kotu da ya hana su shiga yajin aikin da suke yi a fadin kasar.
Shugaban kungiyar Kwadago Festus Osifo ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wata tattaunawa da gidan Talabijin na Channels.
A cewarsa, NLC da TUC ba su samu wani sanarwa ba na umurnin kotu da ya hana ta shiga yajin aikin.
Ba mu da wani umarnin kotu; NLC da TUC ba su da. Babu wata hanyar sadarwa guda daya da zata haifar da hakan”, in ji shi.