Wani Jjirgin kasa da ya taso daga Karachi ta kasar Pakistan ya samu hatsari akan hanya inda aka samu asarar rayuka da kuma wadanda suka samu raunuka da dama
Akalla fasinjoji 19 ne suka mutu sannan wasu sama da 40 suka jikkata bayan wani jirgin kasa ya kauce hanya ranar Lahadi a Pakistan
Jirgin wanda ya tashi daga Karachi, birni mafi girma a Pakistan, motocin jirgin kasa guda takwas sun fita daga kan titin jirgin fasinja kusa da wani gari a lardin Sindh na kudancin kasar, a cewar TheCable
Jami’ai sun ce ana fargabar fasinjoji da dama sun makale a cikin jirgin wanda ke dauke da fasinjoji sama da 1000
KARANTA NANBIDIYO: Yadda Ganduje Da Matarsa Suka Yiwa Maryam Shetty Habaici
An ce jami’an ‘yan sanda da masu aikin ceto suna wurin da hadarin ya afku yayin da aka dakatar da ayyukan jiragen kasa a fadin kasar ta Pakistan mai dumbin Al’umma
Tawagar masu aikin ceto na tura wadanda suka jikkata zuwa asibiti yayin da kuma aka aike da jami’an soji zuwa inda hatsarin ya afku domin taimakawa da ayyukan ceto da kuma agaji
Khawaja Saad Rafique, ministan kula da harkokin jiragen kasa da sufurin jiragen sama na Pakistan, ya ce an sanya dokar ta baci a asibitocin da ke kusa, sannan ya ba da umarnin gudanar da bincike kan musabbabin da ya haddasa hatsarin jirgin
Faduwar jirgin ya Santa wasu wasu a zukatan Al’umma game da amincin layin dogo a Pakistan
A cikin watan Janairu, akalla mutane 15 ne suka jikkata, lokacin da wani bam ya tashi a wani jirgin kasa da ke lardin Balochistan da ke kudu maso yammacin Pakistan
A WANI LABARIN KUMAKu Dawo Bakin Aiki-Gwamna Makinde Ga Ma’aikatan Jahar Oyo
A cikin watan Yunin 2021, aƙalla mutane 63 ne suka mutu lokacin da wani jirgin ƙasa da ke yin rauni ta ƙasar noma ya yi karo da wani sabis ɗin fasinja a lardin Sindh na kudancin Pakistan. An yi la’akari da hadarin a matsayin daya daga cikin mafi munin asarar rayukan jiragen kasa a duniya
Comments 1