Babbar hukumar kasuwar hada-hadar kudi ta Najeriya (NGX) a ranar Talata ta bayyana cewa ta samu Naira biliyan 213 don fara sabon mako bisa la’akari da bukatar masu zuba jari a kamfanin BUA Cement Plc da wasu 23.
Wannan matakin ya zo ne a matsayin martani ga sanarwar rage farashin siminti na kamfanin BUA kwanan nan zuwa Naira 3,500 kan kowace buhu.
Sakamakon haka, NGX All-Share Index (ASI) ya samu jarin kasuwa ya tashi da Naira biliyan 213 inda aka rufe kan Naira tiriliyan 36.544.
Karanta nanAPC Zata Farfado Da Tattalin Arzikin Kano Da Gwamnatin Abba Ta Rusa-Ganduje
Wannan haɓakar ya samo asali ne ta hanyar ƙimar farashi a manyan kamfanonin hannun jari kamar BUA Cement, Beta Glass, UAC of Nigeria (UACN), Oando da Guaranty Trust Holding Company (GTCO).
Kamfanin siminti na BUA ya kasance mafi girman farashin da ya kai kashi 9.94 cikin 100 da aka rufe a kan N94.00, yayin da Beta Glass da FTN Cocoa Processors suka samu kashi 9.93 cikin 100 kowannensu ya rufe a kan N66.95 da kuma N1.66, kowanne kaso.
A wani labarin kuma
Sayen Motoci Masu Aiki Da Iskar Gas:Majalisa Ta Gargadi Tinubu Akan Barnar Kudin Gwamnati
Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya daina batar da kudaden gwamnati barkatai ba tareda lissfai ba.
Wannan kiran dai ya biyo bayan yunkurin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu takeyi wajen sayo manyan motocin jigila na CNG masu amfani da iskar gas domin rage radadin cire tallafin man fetur ga talakawan Najeriya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana daukar wannan matakine a bayanin da yayi a ranar bikin samun yancin kan Najeriya inda ya bayyana cewar akwai matakan da yake dauka wajen magance matsalolin da ke addabar yan Najeriya.