Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu jami’an hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC 8 a kan wata babbar hanya a jihar Zamfara.
An yi garkuwa da mutanen ne a ranar Asabar din da ta gabata, yayin da suke tafiya cikin motar AKTC daga garin Uyo na jihar Akwa Ibom, zuwa jihar Sokoto kan hanyar jihar Zamfara, domin gudanar da aikin yi wa kasa hidima na tilas, a lokacin da motarsu ta tare wata babbar hanya a Zamfara.
Wata majiya a kamfanin sufurin ta bayyana hakan a jiya.
Majiyar wacce ba ta so a ambaci sunanta a cikin rahoton ba saboda ba shi da izinin yin magana kan lamarin, ta ce ‘yan kungiyar sun kai 11 amma uku sun tsere daga hannun ‘yan bindigar.
KARANTA NANJam’iyar PDP Ce Tace In Karbi Mukamin Minista-Wike
Ya ce baya ga masu bautar kasa takwas, an kuma sace direban motar.
An sauke ‘yan kungiyar (daga bas) aka kai su cikin daji. amma yan sanda sun kwato bas din.
Sun bar nan (Uyo) ranar Juma’a, suka kwana a Abuja. A lokacin da suke kan hanyar zuwa Sakkwato ne aka yi garkuwa da su,inji shi.
Ya ce an kai rahoto ga hukumomin gwamnati da hukumomin tsaro.
Wani ma’abocin dandalin sada zumunta na Facebook, Malachy bless, da misalin karfe 9:14 na safe, a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana a shafin Facebook na daya daga cikin wadanda aka sace, Emmanuel Esudue, wanda ya kammala karatun digirin digirgir a fannin aikin gona da muhalli na jami’ar jihar Akwa Ibom.
Ya ce ba a iya samun lambar wayar dan mutumin tun ranar Alhamis.
An bayyana wata mace da abin ya shafa mai suna Betty Udofia.
Wani ma’abocin Facebook Edidiong Richard, ya ce masu garkuwa da mutane sun tuntubi iyayen Ms Udofia, kuma suna neman kudin fansa naira miliyan hudu.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, a jiya, ya ce zai tabbatar da faruwar lamarin sannan ya sanar da wakilinmu inji Jaridar Vanguard
A WANI LABARIN KUMAGwamnatin Jahar Katsina Ta Kaddamar Da Asusun Bai Daya Domin Hana Satar Kudin Al’umma
Hakazalika, mai magana da yawun hukumar NYSC, Eddy Megwa, bai amsa kiran da aka yi masa a layin wayarsa ba har zuwa lokacin da aka buga labarin.