Kungiyar koli ta al’adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta yi kira ga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, da ya yi ritaya daga siyasa a 2023.
Ohanaeze sunce burin Atiku na zama shugaban kasa ya zo karshe.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a lokacin da take yabawa Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Minista, Nyesom Wike a karkashin jagorancin Gwamnonin G-5 da suka ruguza burin Atiku na zama shugaban kasa.
Karanta nanGwamnonin Zamfara Na Boye Hakikanin Gaskiyar Rashin Tsaro A Jahar-Marafa
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar Ohanaeze, Okechukwu Isiguzoro, ta ce ya kamata Atiku ya yi ritaya daga siyasa saboda ya yi watsi da tsarin shiyya-shiyya a zaben shugaban kasa da ya gabata.
Ya kuma yabawa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, shugaban Afenifere, Ayo Adebanjo, wanda ya goyi bayan jam’iyyar Labour Party, LP, dan takarar shugaban kasa, Peter Obi.
Sanarwar ta kara da cewa muna mika godiyarmu ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, da Pa Ayo Adebanjo-Afenifere, da Dr Pogu Bitrus, Middle Belt Forum, Pa Edwin karkashin jagorancin Pan Niger Delta (PANDEF), da sauran duk wadanda suka tsaya tsayin daka. domin goyon bayan Mista Peter Obi. Jajircewarsu ba tare da kakkautawa ba abin a yaba ne.
An mika godiya ta musamman ga Gwamnonin G5 karkashin jagorancin Nyesom Wike saboda rawar da suka taka wajen ruguza burin Atiku Abubakar da Jam’iyyar PDP.
A wani labarin kumaRasuwar Dr Adamu Fika Babban Gibi Ne Ga Al’ummar Jahar Yobe-KACRAN
Burin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na zama shugaban kasa ya zo karshe inji Ohaneaze.
Yanzu ne lokacin da ya dace da ya yi ritaya daga siyasa cikin ruwan sanyi sanin cewa burinsa na dawo da Jam’iyar PDP wadda ya ruguza cikin hayacinta ba zai cika ba a yanzu.