Wani Lauyan kasar Kenya Paul Gicheru da ke fuskantar shari’a a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ya mutu kamar yadda iyalansa da yan sanda suka tabbatar wa kafafen yada labaran kasar. Kamar yadda BBC ta ruwaito
Rundunar yan sanda kasar ta ce an tsinci gawar Mista Gicheru a gidansa da ke Nairobi babban birnin kasar a daren jiya Litini.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Jam’iyyar APC Ta Dakatar Da Wani Dan Majalisa A Jigawa
Ana zargin Mista Gicheru da bayar da cin hanci ga shaidun da za su ba da shaida kan William Ruto wanda a yanzu shi ne shugaban kasar kenya kan rikicin da ya biyo bayan zaben Kenya daya gudana a 2007 zuwa 2008 wanda aka samu hasarar rayuka sama da mutun 1,000 amma duk da haka ya musanta zargin.
Lauyan ya mika kansa ga kotu ne a watan Nuwambar 2020, shekaru biyar bayan kotun ICC ta bayar da sammacin kama shi.
A WANI LABARIN KUMA: An Gargaɗi Tinubu Da APC Kan Amfani Da Kuɗi Wajen Raba Kan Kiristoci
An gargadi jam’iyyar APC mai mulkin kasa, da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, da kada su haifar da rabuwar Kawuna Tsakanin Kiristoci ta hanyar amfani da kudi.
Gargadin ya fito ne a cikin wata sanarwa da kungiyar dattawan kiristoci ta jihohin Arewa ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Oyinehi Inalegwu, a ranar Talata.