An tsinci Gawar wani Mutum cikin Tankin dizal a Kano
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta dauko gawar wani mutum a ranar Litinin.
An fito da gawar ne daga tankin dizal a wani kamfani dake karamar hukumar Kumbotso.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ina Da Kyakkyawan Zaton Yan Arewa Zasu Zazzagawa Tinubu ƙuri’un Su – Sanata Uba Sani
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara, Saminu Abdullahi ya bayyana cewa mamacin na riƙe da jarkar a hannunsa.
Kakakin ya ce hukumar ta amsa kiran gaggawar da mazauna yankin suka yi musu.
Likita ne ya tabbatar da mutuwar mutumin bayan an mika gawar ga ofishin ‘yan sanda na Panshekara da ke Kano.
“Kokarin gano shi ya ci tura domin jami’an tsaro a kamfanin sun ce ba su san shi ba,” Abdullahi ya kara da cewa.
A wani labarin kuma: Karim Benzema ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2022
Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2022 bayan ya yi murnar shekara mai ban mamaki.
Dan wasan na Faransa ya doke Mohamed Salah da Robert Lewandowski da Sadio Mane da Kylian Mbappe da kuma Erling Haaland inda ya samu kyautar kyautar gwal.