- An gurfanar da wasu kananan yara uku a gaban wata kotun Majistare dake Ado-Ekiti bisa zargin su da hallaka wani dawisu
- Wadanda ake tuhumar an tuhume su da laifin yin keta da kuma barna
- Alkalin kotun, Misis Kehinde Awosika, ta amince da bayar da belinsu a kan kudi naira 50,000 kowannen su
A ranar Juma’a ne aka gurfanar da wasu kananan yara uku a gaban wata kotun Majistare dake Ado-Ekiti bisa zargin su da hallaka wani dawisu.
Wadanda ake tuhumar, wadanda ba a bayyana adireshinsu ba, an tuhume su da laifin yin barna.
KARANTA WANNAN: Babu Wani Ɗan Filato da Zai Kara Jikkata Sanadiyyar Rikici – Gwamna Mutfwang
Lauyan masu shigar da kara, Insifekta Olubu Apata, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 11 ga watan Yuni a Usi-Ekiti.
Apata ya yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun kashe wani dawisu da kudin sa ya kai Naira miliyan 1 mallakin wani Agbetuyi da nufin sace shi.
Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 421 da na 306 na dokokin laifuka na jihar Ekiti, shekarar 2021.
Lauyan mai gabatar da kara ya roki kotun da ta dage shari’ar domin ya yi nazari kan fayil din karar tare da gabatar da shaidunsa.
Sai dai wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.
Lauyan wadanda ake kara, Mista Eric Omotoso, ya bukaci kotun da ta bayar da belin wadanda ake zargi.
Alkalin kotun, Misis Kehinde Awosika, ta amince da bayar da belinsu a kan kudi naira 50,000 kowannen su da mutum daya da zai tsaya musu.
Ta dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 17 ga watan Yuli domin sake sauraren karar.(NAN)
A wani labarin kuma, Wani Gwamna Ya Bayar Da Umarnin Dakatar Da Ayyukan Hakar Ma’adinai A Jihar sa
Gwamna Kefas na jihar Taraba ya umurci
masu hakar ma’adanai a fadin jihar da su nemi wata hanyar rayuwa ko kuma su fuskanci fushin doka
Da yake rattaba hannu kan dokar da ta haramta hakar ma’adanai a jihar,gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta nade hannayenta ba, tana kallon yadda ake lalata albarkatun kasa
Haramta irin wadannan ayyuka zai taimaka matuka wajen magance wasu matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta a halin yanzu