- An yiwa ‘yan Najeriya rijistar haihuwa sama da miliyan 1,174,392 a fadin kasar nan.
- Muna kara wayar da kan jama’a daga hukumar domin ganin ‘yan Najeriya sun yi rajistar ‘ya’yansu a lokacin haihuwa.
- NPC tace suna hada kai da hukumomin kiwon lafiya a matakin farko da sauransu hukumomin da suka dace wajen yada sakon rajistar yin haihuwa ga ‘yan Najeriya.
An yiwa ‘yan Najeriya rijistar haihuwa sama da miliyan 1,174,392 a fadin kasar tsakanin watannin Janairu zuwa Mayun 2023.
Wannan adadi yana kunshe ne a cikin wata manhaja mai suna RapidSMS da hukumar kula da yawan jama’a ta kasa ta tsara kuma wakilinmu ya samu a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN: Majalisar Shari’a Ta Yi Martani Ga CAN Kan Kalaman El-Rufa’i
Punch ta rawaito cewa RapidSMS yana aiki azaman hanyar tattara bayanai da dandamali don rijistar haihuwa ta yanar gizo da kuma wadda bata yanar gizo ba.
A cewar manhajar, rijistar haihuwar yara a karkashin daya ya kai guda 362,798; Yara ‘yan kasa da shekara biyar sun kasance guda 562,345; da kuma yara ‘yan sama da shekaru biyar sun kasance guda 249,249.
An yi wa yara mata 580,820 rajista yayin da aka yiwa maza guda 593,572 rajista.
Manhajar ta kara da cewa an yiwa yaran mata rajista a cibiyoyi 2,573 yayin da mazan aka yi musu rijista a cibiyoyi 3,936 a fadin kasar nan.
A cewar manhajar, an yiwa yara guda 304,118 rajista a watan Janairu; sannan guda 142,142 a watan Fabrairu; haka kuma guda 267,583 a watan Maris; kazalika guda 228,456 a watan Afrilu; da kuma 232,093 a watan Mayun 2023.
Manhajar ta bayyana cewa jihar Legas ce ta fi kowacce jiha yawan wadanda aka yiwa rijistar haihuwa 115,264, sai Ogun mai guda 82,296; da kuma Bauchi mai rajistar haihuwa guda 76,767.
Sauran jihohin sun hada da; Filato guda 45,421; Zamfara guda 6,687; Yobe 13,109; Taraba 25,643; Sokoto 65,499; Rivers 32,095; Oyo 42,036; Neja 15,352; Nasarawa 9,545; Kwara 53,730; Kebbi 4,753; Katsina 41,096; Imo 14,983; Kano 10,693; Kaduna 17,641; Jigawa 7,462; Gombe 4,650; Enugu 5,330; da Ebonyi mai rijistar haihuwa guda 27,004.
Kazalika sai Delta mai rijistar haihuwa guda 37,467; Cross-River 12,732; Borno 67,416; Benue 38,009; Akwa-Ibom 24,181; Adamawa 33,796; Anambra 36,898; Bayelsa 9,440; Edo, 53,490; Ekiti 22,048; Ondo 25,568; Osun 28,615; Babban Birnin Tarayya 26,768; Kogi 25,522; da kuma jihar Abia mai rijistar haihuwa guda 26,058.
Da yake zantawa da wakilinmu a ranar Lahadin da ta gabata, Daraktan Rijista na NPC, Matthew Sunday, ya bayyana cewa ana ci gaba da kara wayar da kan jama’a daga hukumar domin ganin ‘yan Najeriya sun yi rajistar ‘ya’yansu a lokacin haihuwa.
Sunday ya ce, “Ka’idar ta yi tasiri sosai kuma ana samun sabuntawa daga lokaci zuwa lokaci.
“Mun yi taka-tsan-tsan da fadakarwa don sanar da ‘yan Najeriya mahimmancin yin rajistar haihuwa.”
“UNICEF ta kasance babban ginshikin tallafi a wannan shawarwarin. Muna hada kai da hukumomin kiwon lafiya a matakin farko, kungiyar masu yi wa kasa hidima, da hukumar wayar da kan jama’a don taimaka mana wajen yada sakon rajistar yin haihuwa ga ‘yan Najeriya.”
A wani labarin kuma,Kai Maƙaryaci Ne, Dan Majalisar Da Sirika Ya Zarga Ya Mayar Da Martani
Tsohon shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin jiragen sama, Honarabul Nnolim Nnaji, ya zargi Sanata Hadi Sirika, tsohon ministan sufurin jiragen sama da yi masa karya.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga zargin da tsohon ministan sufurin jiragen sama ya yi masa.