Ana cigaba da tada jijiyar wuya kan shirin Kwankwasiyya na mamaye Kotun Koli
Gamayyar kungiyoyin farar hula ta dimokaradiyya ta koka kan shirin da kungiyar Kwankwasiyya ta yi na mamaye harabar kotun koli da ma’aikatun kasashen waje a kasar nan gabanin yanke hukuncin zaben gwamnan jihar Kano.
Sakataren kungiyar na kasa Otunba Eniola Enaife ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kotu Za Ta Rataye Wanda Ya Kashe Abokinsa Akan Naira 10,000 A Zamfara
Ya ce kungiyar ta kuduri aniyar yin tir da duk wani nau’i na tsoratarwa, da kuma bakaken maganganu ga shugaban kasa Bola Tinubu da bangaren shari’a.
Don haka kungiyar ta yi kira ga babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun da ya gaggauta kamo dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party a zaben 2023 kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya ci gaba da cewa: “Lokacin da za a kama Kwankwaso da wani Ladipo Johnson, wani dan kasuwan rikicin da ke aiwatar da mafi yawan hare-haren, ya yi. A shirye suke su mayar da kasar ba ta da mulki don biyan bukatunsu.
“Ba shakka muna kira ga Sufeto Janar na ‘yan sanda da ya tashi tsaye wajen daukar nauyin da ya rataya a wuyansa na kame Mista Rabi’u Musa Kwankwaso saboda halin da yake ciki na bata sunan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da bangaren shari’a ta hanyar haddasa yakin kabilanci da addini a kasar nan ya kara bayyana a yanzu.
“Sun shirya mamaye harabar kotun koli da ma’aikatun kasashen waje a kasar nan duk da cewa kwamitin amintattu na NNPP a wata ganawa da manema labarai ya amince da cewa Engr. Abba Kabir Yusuf ba dan jam’iyyarsu ba ne a lokacin da aka zabe shi Gwamnan Jihar Kano.”
Kungiyar ta yi zargin cewa kungiyar Kwankwasiyya na shirin kai wa fitattun ‘yan jam’iyyar APC hari a ciki da wajen jihar Kano.
Ta ce dole ne jami’an tsaro su dakile wannan aika-aika, kafin ya fita daga hannu.