A jiya ne dai aka samu tashin hankali a Unguwar Yero da Badarawa Kwaru da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa sakamakon mutuwar wani matashi a yankin.
Daily Trust ta ruwaito cewa ’yan banga na yankin ne suka azabtar da marigayin a Unguwar Yero bayan sun kama shi da wuka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilan Da Suka Naki Amsar Kyautar Lambar Yabon Shugaba Buhari— Kaigama
Lamarin ya faru ne da misalin karfe tara na safe, kuma marigayin ya rasu ne a asibitin da yake jinya.
Majiyar Dimokuradiyya a ranar Asabar din da ta gabata ta tattaro cewa mutuwar tasa ta fusata wasu matasa ‘yan kabilarsa dake zaune a Badarawa Kwaru yayin da suka kuma daba wa wani matashi dan unguwar Unguwar Yero wuka a matsayin ramuwar gayya.
Wani shugaban matasa a yankin wanda ya bayyana kansa a matsayin Mohammad Mohammed ya ce an tura jami’an tsaro yankin domin tabbatar da doka da oda.
Rahotanni sun nuna cewa al’ummomin biyu na da tarihin rikicin addini da na kabilanci a jihar.
Lamarin na baya-bayan nan ya kusa daukar wani sabon salo na kabilanci idan ba don shigar da jami’an ‘yan sanda daga rundunar Operation Yaki ba.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, wanda ya yi alkwarin mayar da martani bayan samun cikakken bayanin abin da ya faru daga jami’in Daan sandan dake kula da yankin, bai sake kira ba kuma bai amsa kiran wayar da aka masa ba harzuwa lokacin hada wannan rahoton
A WANI LABARIN KUMA: Ku Dauki Kwararrun Ma’aikata– An Ja Kunnen INEC
An bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta dauki kwararrun ma’aikata da tabbatar da isar da muhimman abubuwa a kan lokaci zuwa kowane lungu da sako na jiha da kasa baki daya.
Shugaban kungiyar Unified Nigerian Youth Forum (UNYF), Kwamared Abdulsalam Mohammed Kazeem ne ya bayyana hakan, a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a Kaduna, ya kara da yin kira ga ‘yan kasar nan da su tashi tsaye tare da marawa hukumar ta INEC baya domin ganin an gudanar da zaben 2023 lami lafiya