Wani zaƙakurin ango ya shirya angwancewa da mata 4 rigis a lokaci ɗaya.
Angon mai suna Nasiru Hamisu ya shirya angwancewa a Ranar Lahadi 14 ga watan nan na Mayu na wannan shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN : Wani matashi da ya killace kansa har na tsawon awanni ashirin da huɗu 24 ba tare da ya fita wajen ɗakin da yake ciki ba, ba kuma tare da ya ɗauki wayar sa ta hannu ba, ya samu ƙyautar Naira dubu hamsin 50,000 dai-dai.
Haziƙin angon zai angwance da amaren nasa masu suna Fatima Abubakar, Ummulkhairi Musa, Fatima Kanel sai kuma Na’ima Nasir.
Hoton katin gayyatar ɗaurin auren ya bayyana ne a shafukan sada zumunta na zamani wanda kuma yaja hankulan mutane da dama a shafukan sada zumunta daban daban.
Wasu da suka bibiyi hoton katin gayyatar ɗaurin auren jajirtacce kuma haziƙin ango Nasiru, sun bayyana shi a matsayin Jarumin Maza… Ɗaya Tamkar Da Dubu. Yayin da wasu kuma ke tambayar ko wace ce a cikin matan da zai aure zata fara kasance a ɗakinsa kuma wace ce zata biyo bayanta.
Wasu kuma a nasu ɓangaren addu’ar zaman lafiya da ƙoƙorin kwatanta adalci suka yi wa Jarumi Nasir.
A WANI LABARIN KUMA:
Shahararren ɗan wasan kwaikwayon Kannywood ɗin nan da aka fi sani da Adam A. Zango ya ce yana tunanin auren kirista a matsayin matarsa.
Adam zango ya wallafa hakan ne a shafinsa na sada zumuntar zamani na Instagram yana me buƙatar neman shawarar auran kiristan ga masu bibiyar shafin nasa.
Zango wanda yake ta fama da matsalolin aure, wanda da yawa mutane suke cewa bu yana da auri-saki sakamakon yawan aure da yake yi sannan kuma babu jimawa sai ya saki wacce ya aura.
A baya dai, idan za ku iya tunawa, fitaccen jarimin masana’antar Kannywood ɗin yayi wani furuci da ya yamutsa hazo musamman a shafukan sada zumunta daban-daban inda yace shi ya haƙura da aure gabaki ɗaya har karshen rayuwar sa.
Wannan furucin da yayi ya biyo bayan saɓanin da ya yake samu da matarsa wanda yayi dogon bidiyo ya kuma bayyana hakan ta cikinsa.