Jam’iyyar APC a Jihar Katsina Ta Fitar Da Kuɗin Form Na Masu Sha’awar Tsayawa Takarar Neman Shugabancin Kananan Hukumomin Da Kansila AJihar.
Kamar yadda jaddawalin farashin kudin form din ya nuna:
Shugaban Karamar Hukuma Naira Dubu Dari Bakwai Da Hamsin (750,000).
Dan Takarar Kansila Naira Dubu Dari Da Hamsin (150,000).
KARANTA WANNAN LABARIN: An Dage Sauraren Karar Wanda Ya Kashe Hanifa, Yayin Da Kotu Ta Iza Keyarsu Gidan Yari
Bayan Waɗannan Kuɗin Fom Na Jam’iyyar APC Akwai Na Nuna Sha’awar Tsayawa Takarar Inda Shugaban Karamar Hukuma Zai Biya Naira Dubu Hamsin 50,000.
Sai Shi Kuma Dan Takarar Kansila Zai Biya Naira Dubu Goma Sha Sha Biyar 15,000.
An dai sanar da hakan ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da Gwamna Aminu Bello Masari ya Jagoranta.