Jam’iyyar APC ta sauya ranar taron kaddamar da kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar ta mai mambobi 422.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa tun da farko jam’iyyar ta shirya yi a ranar Litinin 26 ga watan Satumba, inda yanzu kuma aka sauya shi zuwa Laraba 28 ga watan Satumba.
Mista Bayo Onanuga, Daraktan Yada Labarai na kwamitin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Lahadi a Abuja.
KARANTA ANAN: Rashin Tsaro: Najeriya Na Cikin Mawuyacin Hali ~UN
”Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC na son sanar da duk mambobin da aka zaba domin yin aiki a daraktoci daban-daban da su kai rahoto hedikwatar yakin neman zaben ranar Laraba 28 ga Satumba, 2022 da karfe 8 na safe.”
Ya taya mambobin kwamitin yakin neman zaben murna, inda ya ce kira ne da su yi wa jam’iyyar hidima da sadaukarwa.
Ya ce jam’iyyar APC da ’yan takarar sun amince da kwazon da suka yi da dimbin kudi da na ma’aikata da aka kashe ba tare da nuna don rai ba.
A wani labarin kuma: Zanga-zangar ‘Ayu Ya Tafi’ Wasu Ne Daga Waje Suka Dauki Nauyinta – Shugaban PDP Na Katsina, Majigiri
Shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Katsina, Alhaji Salisu Majigiri ya ce masu zanga-zangar “Ayu Must Go” da suka mamaye babban birnin jihar Katsina a ranar Lahadin da ta gabata, tabbas makiya jam’iyyar daga wajen jihar ne suka dauki nauyinsu.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito a ranar Lahadin da ta gabata cewa, an ga wasu gamayyar matasan Arewa, wadanda aka ce ‘yan PDP ne dauke da alluna a kofar shiga birnin Katsina, suna neman shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya gaggauta yin murabus.