- Jam’iyyar APC ta fitar da jerin sunayen mutane 582 na kwamitin yakin neman zabenta na gwamnan Imo
- APC ta ce gwamnan Cross River ne zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben
- INEC ta ce za a gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 11 ga watan Nuwamba
Jam’iyyar APC ta fitar da jerin sunayen mutane 582 na kwamitin yakin neman zabenta na gwamnan jihar Imo, Daily Post ta rawaito.
Jadawalin lokaci da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar, ta ce za a gudanar da zaben gwamnan jihar Imo a ranar 11 ga watan Nuwamba.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: An Cafke Wasu Jami’an Sojoji 3 Bisa Laifin Kitsa Juyin Milki a Burkina Faso
Sai dai APC ta ce gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Riba ne zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben.
Wani sakon Tweeter da jam’iyyar mai mulki ta wallafa ya bayyana cewa za a kaddamar da kwamitin yakin neman zaben ranar Asabar 16 ga watan Satumba a Owerri, babban birnin jihar Imo.
A cewar APC: “BAYANAN JERIN SUNAYEN: Gwamnan Jihar Kuros Riba, H.E. Bassey Edet Otu shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar mai wakilai 582 a zaben gwamnan Imo na ranar 11 ga watan Nuwamba.
“Za a yi bikin kaddamarwar ne a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba, a Landmark Event Centre dake Owerri, da karfe 11 na safe.”
A wani labarin kuma, Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Yi Bikin Cika Kwanaki 100 Da Fara Mulki Ba – Gwamnan Neja
Gwamnan Neja, Mohammed Bago, ya bayyana dalilan da suka sa ba zai yi bikin cika kwanaki 100 da ya yi yana mulki ba
Tarihi siyasa ya nuna cewa duk abin da ba a rubuta shi ba, ko dai ba za a lura da shi ba, ko kuma a manta da shi cikin sauki
Gwamnatin gwamnan ta fara ne da bayyana wasu muhimman wurare da za su zama ginshiki da karfi da gwamnatin za ta tsaya a kai
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago, ya bayyana dalilan da suka sa ba zai yi bikin cika kwanaki 100 da ya yi yana mulki ba.
Gwamnan, wanda ya yi ikirarin cewa ba ya son shiga ayyukan gyaran tagogi don nuna nasarorin da ya samu, ya kara da cewa ya fi son nuna ayyuka masu inganci da za su dore, don haka ya mayar da hankali da himma wajen gina “Sabuwar jihar Neja” wanda kowa zai so.