APC ta mayar da zazzafan martani ga Gwamnatin NNPP kan zargin cin hanci
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Alhamis ta gargadi gwamnatin jam’iyyar New Nigeria People’s Party reshen jihar Kano da ta yi watsi da kama sunan shugabar kotun sauraren kararrakin zabe ta ƴan majalisa da ta Jiha, Mai shari’a Flora Azinge, saboda rashin tsaro a kotun.
Jam’iyyar APC ta ce yunkurin da gwamnatin jihar Kano ta yi da gangan na zargin shugaban kotun saboda tsoron abin da ka iya zama hukunci na karshe, ta hanyar kirkiro labarin karya tare da ba da labarin ba tare da wani dalili ba, ya kai ga rashin mutunta alkali da bangaren shari’a gaba daya.
KARANTA WANNAN LABARIN:ZARGIN LALATA: Jami’ar Jihar Calabar ta kori malaminta
Wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida kuma kakakin majalisar yakin neman zaben Gawuna/Garo, Mallam Muhammad Garba ya fitar ta bayyana cewa “lokacin da Hon. Mai shari’a Azinge ta bayyana hakan ne a kan yunkurin da wani babban lauya ya yi na bata cin hanci, ba ta bayyana sunan kowacce jam’iyya bace ba.”
“Wannan matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka ba komai ba ne illa yaudara da kuma yunkurin tozarta jam’iyyar APC,” inji shi.
A cewarsa, amma don kawai a tozarta APC, gwamnatin NNPP ta kira APC a matsayin mai bayar da cin hanci.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kuma yi tanadin yiwuwar bankado ainihin mai bayar da cin hancin da kotun ta yi, don haka ta bukaci a tuhumi alkalin.
Garba ya kuma ce, zargin da kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Dantiye ya yi, ya kara da cewa gwamnati na kokarin yi wa kotun zagon kasa ne kafin yanke hukunci domin ta jajanta wa jama’ar da ba su san komai ba idan aka ci ta.
A wani labarin kuma:Sabbin Manufofin Kasuwar Canjin Kudade Tsohon Labari ne, CBN ya Magantu
Babban bankin Najeriya CBN ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa ya bullo da wasu sabbin tsare-tsare a kasuwar canjin kudade
CBN yace an wallafa wannan rahoton ne wanda a yanzu ke yawo a shafukan sada zumunta tun a shekarar 2017