’Yan jam’iyyar APC a shiyyar Enugu ta yamma sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP domin marawa dan takararta na gwamna Barista Peter Mba baya, Daily Post ta rawaito.
‘Yan jam’iyyar APC sun kona tsintsiya madaurinki daya a lokacin da suke rungumar jam’iyyar PDP a wajen taron amincewa da aka shirya a shiyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin Naira: APC ta Bukaci FG, CBN Su Bi Umarnin Kotu, Sun Nemi Buhari Ya Sanya Baki
Sun bayyana PDP a matsayin kawai fatan Enugu na kyakkyawan shugabanci.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Kananan hukumomi biyar da ‘yan jam’iyyar APC suka sauya sheka sun kunshi shiyyar Sanatan Enugu ta Yamma sun hada da Aninri, Awgu, Ezeagu, Kogin Oji da Udi.
Masu sauya shekar, wadanda tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC a jihar, Mista Gilbert Chikwado-Chukwu ya jagoranta, sun bayyana rashin amincewarsu da jam’iyyar APC, inda suka bayyana matakin nasu na tarihi da kuma samun haske da fata.
Chikwado-Chukwu wanda ya yi magana a madadin sauran ya ce sun yanke shawarar shiga jam’iyya mai mulki ne saboda kyakkyawan shugabanci da dimbin ababen more rayuwa da jihar ke samu a karkashin jam’iyyar.
Da yake karbar tsoffin ‘ya’yan jam’iyyar APC zuwa PDP tare da mika musu laima, shugaban jam’iyyar na jihar, Augustine Nnamani ya yaba musu bisa daukar matakin da ya dace, ya kuma ba da tabbacin cewa jam’iyyar PDP za ta ba su duk wani gata da ‘ya’yan kungiyar ke samu.
A wani labarin kuma, Rashin Ilimi na Da Alhakin Kashi 80 Na Kalubalen Da Najeriya Ke Fuskanta
Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe ya dora alhakin kashi 80 cikin 100 na kalubalen da Najeriya ke fuskanta kan rashin samun ilimi daga al’ummar kasar.
Ortom ya bayyana haka ne a karshen makon da ya gabata a jawabinsa yayin taron hadakar dalibai hudu da suka kammala karatu a jami’ar jihar Benue (BSU) da ke Makurdi.