Dan takarar jam’iyyar APC, Mista Abdullahi Lado na mazabar Suleja, Tafa da Gurara, ya sha kaye a zaben da ya gabata a hannun dan takarar jam’iyyar PDP, Tanko Adamu.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa Lado shi ne mamba mai wakiltar mazabar Suleja/Tafa/Gurara a yanzu.
Jami’in hukumar INEC, Tanimu Garba a lokacin da yake sanar da sakamakon zaben ya ce dan takarar PDP ya samu kuri’u 40,632 inda ya doke dan takarar APC da ya samu kuri’u 38,217.
KU KARANTA KUMA An Bada Horan Aikin Tsaro Ga Jami’an Sa Kai Na Garin Suleja
Garba ya bayyana dan takarar PDP ne bayan ya cika sharuddan doka kuma ya ci zabe.
Sauran ‘yan takarar sun hada da George James na ADC wanda ya samu 344 yayin da Ibrahim Ibrahim na ADP ya samu 231 sai Tanko Ahmed na APGA ya samu 979 haka kuma Yusufu Muhammed na APP ya samu 94 yayin da dan takarar jam’iyyar Labour ya samu 19,219.
Haka kuma, dan takarar jam’iyyar NNPP ya samu 1,255, NRM ta samu 101, PRP ya samu 145, SDP ya samu 46, Isah Jagaba na ZLP ya samu kuri’u 297.
Hakazalika, an ayyana Alhaji Abdullahi Maud na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar tarayya ta Agaie/Lapai.
Maud ya samu kuri’u 29,671 inda ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 25,439 sannan dan takarar NNPP ya samu kuri’u 2,157. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Walin Kazaure Ya Lashe Kujerar Sanatan Jigawa Ta Arewa Maso Yamma
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC Dr. Babangida Hussaini a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar.
Zaben na shekarar 2023, ya samu nasara a shiyyar Jigawa ta arewa maso yamma.