…Jam’iyyar APC reshen jihar Gombe ta kaddamar da wani kwamiti da zai binciki zrgin da ake yiwa sanata mai ci kan.
Jam’iyyar APC reshen jihar Gombe, ta kaddamar da wani kwamiti mai mutum 5 da zai binciki zargin yiwa Sanata Danjuma Goje na yiwa wata jam’iyyar aiki a zaben 2023.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Tanimu Abdullahi, shugaban jam’iyyar APC a mazabar Kashere ya bayyana haka a garin Kashere da ke karamar hukumar Akko a lokacin da ya kaddamar da kwamitin a ranar Laraba.
Mista Abdullahi ya ce bikin kaddamarwar ya yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar, wanda ya tanadi yin gaskiya da adalci.
KARANTA HAKANAN Rashin Goje a Kamfen Din Shugaban Kasa Ya Kawo Cikas Ga APC
Ya ce ana zargin Mista Goje da magoya bayansa da taimakawa wata jam’iyyar adawa a jihar a lokacin zaben da aka kammala.
“A lokacin zaben da aka kammala, abin takaici ne yadda Danjuma Goje da magoya bayansa suka tsunduma cikin adawa da jam’iyya kuma dukkan mu shaidu ne.
“Ya ba wa wasu ‘ya’yan jam’iyyar umarnin zaben wata jam’iyya ta daban kuma ya ci gaba da ba da kudi ga wannan tsari.
“Ya kamata ya zama misali da ya dade yana cin gajiyar jam’iyyar amma ya saba wa jam’iyyarmu; wannan abin takaici ne,” in ji Mista Abdullahi.
Ya ce an ba kwamitin wa’adin kwanaki 14 da ya mika shawarwarinsa ga jam’iyyar a matakin mazaba domin daukar matakin da ya dace.
‘’ Ana sa ran kwamitin zai bankado duk wadanda ke da hannu a ciki kuma za su yi amfani da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar bisa ga sakamakon binciken da zasu gudanar,’’ inji shi.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Shugaban gundumar ya ce kaddamar da kwamatin ya kuma kasance bisa tsarin tabbatar da gaskiya da adalci da daidaito bisa tsarin mulkin jam’iyyar. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Kogi Ya Yi Murabus
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kogi, Muktar Bajeh a ranar Alhamis ya sanar da yin murabus daga mukaminsa.
Dan majalisar ya ce ya yi murabus ne saboda wani nauyi da ya rataya a wuyana a nan gaba wanda ke bukatar kulawa ta cikin gaggawa.