APC za ta lashe Zaɓen 2023 a Kudu Maso Gabas – Uzodinma
Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma ya ce jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben 2023 a yankin Kudu maso Gabas.
Gwamnan ya bayyana cewa ita ce jam’iyya daya tilo da ke da tsari a ɗaukacin Ƙananan Hukumomi 774 na Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba Mu Da Hannu a Satar Mai – Sojoji
Uzodinma, Shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a shiyyar Kudu-maso-Gabas, ya yi magana a ranar Alhamis a wajen wani taron karawa juna sani na ƴan takarar jam’iyyar.
“APC ta riga ta yi nasara kuma za ta yi nasara a Kudu maso Gabas”, in ji shi a Owerri.
Uzodinma ya ce taron karawa juna sani an yi shi ne domin a samu nasarar yakin neman zaben gabanin zaben.
Ya shawarci mahalarta taron da su ɗauki jam’iyya da magoya bayansu domin ba za su iya cin zaɓe su kaɗai ba.
Gwamnan ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi ayyuka da dama a shiyyar tun bayan hawansa mulki.
Ya lissafta gadar Neja ta biyu, gyaran manyan titunan Gwamnatin Tarayya, kafa sansanin sojin ruwa a Ƙaramar Hukumar Oguta, da aikin sake gina Asibitin Koyarwa na Jami’ar Imo da ke Orlu da dai sauransu.
Uzodinma ya shaidawa ƴan ƙabilar Igbo cewa kada su fadi zaben wadanda ke shelanta shugabancin yankin Kudu maso Gabas amma ba su goyi bayan masu neman shiyyar ba a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.
Shugaban na Imo ya kara da cewa, “Akwai bukatar Kudu-maso-Gabas su ɗauki makomarsu a hannunsu”.
A wani labarin kuma: IPOB ta zargi Asari Dokubo da Ɗaukar nauyin kashe-kashe a Kudu maso Gabas
Kungiyar Masu Fafutukar Kafa Ƙasar Biafra (IPOB) ta zargi tsohon shugaban tsagerun, Asari Dokubo da hada baki da ake zarginsa da kashe ƴan asalin jihar Imo da wasu yankunan Kudu maso Gabas.
Kakakin Ƙungiyar ƴan awaren, Emma Powerful ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.