Hukumomi a kasar Saudiyya sun bayyana cewa bana za a gudanar da itiƙafi a Masallatan Harami lokacin azumin watan Ramadan.
Shafin Haramain Sharifain ya rawaito cewa nan gaba kadan ne za a fitar da tsarin gudanar da itiƙafi a shafin yanar gizo na hukumar da ke kula da masallatan biyu.
Wanna ne karon farko da za a gudanar da itiƙafi cikin shekaru biyu tun bayan bullar annobar cutar korona a kasar ta Saudiyya da wasu kasashen duniya.
A wani labarin Kuma na daban
A ranar Talata ne dai ‘yan sanda suka tare kofar shiga rukunin majalisar dokokin jihar Cross River da ke Calabar, biyo bayan hukuncin da wata kotu ta yanke ranar Litinin na korar ‘yan majalisa 20 a jihar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ma’aikatan majalisar da wasu da ke da sana’o’in da za su yi mu’amala da su a harabar, an hana su shiga harabar da ke daura da U.J. Esuene Stadium.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Irene Ugbo, ta shaida wa NAN cewa, matakin da suka dauka shi ne don dakile duk wani abu da ka iya faruwa, biyo bayan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a Abuja.
A ranar Litinin ne mai shari’a Taiwo Taiwo ya kori ‘yan majalisar jihar 20 da suka hada da ‘yan majalisar wakilai biyu na tarayya da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC.
‘Yan majalisar dai sun fice daga jam’iyyar PDP ne tare da Gwamna Ben Ayade, wanda ya ce ya koma jam’iyya mai mulki ne domin marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya domin gina kasa gaba
Hukuncin Taiwo, ya biyo bayan karar da jam’iyyar PDP ta shigar na neman a tsige ‘yan majalisar dokoki na kasa da na jiha wadanda suka sauya sheka daga PDP zuwa APC. (NAN)
Lamarin dai na zuwa ne makonni kadan bayan da kotu ta kori Gwamna David Umahi na Ebonyi da mataimakinsa da wasu ‘yan majalisar dokokin jihar saboda sauya sheka.