- Jam’iyyar APC reshen jihar Rivers ta musanta cewa ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike zuwa cikin jam’iyyar
- APC ta bayyana wadanda ke ikirarin neman Wike ya koma jam’iyyarsu a matsayin masu yin zagon kasa
- APC ta ce Wike ya ji kunyar shiga jam’iyyar da ya bayyana a matsayin ciwon daji
Jam’iyyar APC reshen jihar Rivers ta musanta cewa ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike zuwa cikin jam’iyyar, kamar yadda Daily Post ta rawaito.
APC ta bayyana wadanda ke ikirarin da kuma kiran Wike ya koma jam’iyyarsu a matsayin masu yin zagon kasa.
KARANTA WANNAN: Kano: NDLEA Ta Kama Mutane Tare Da Haramtattun Kwayoyi
Jam’iyyar a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jihar, Darlington Nwauju ya fitar, ta ce Wike ya ji kunyar shiga jam’iyyar da ya bayyana a matsayin ciwon daji.
Nwauju ya ce ta’addancin da aka yi wa ‘ya’yan jam’iyyar APC a lokacin gwamnatin Wike ya isa shaida da ke tabbatar da cewa Wike ba shi da wata alaka da APC a jihar Ribas.
Don haka Kakakin jam’iyyar APC ya nesanta shugabannin jam’iyyar daga duk wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda ya nuna cewa a mika jam’iyyar da alfanun ta ga Wike.
Ya kuma jajircewa kowa ya bayar da hujjojin bidiyo na Wike na yakin neman zabe karara ga jam’iyyar APC a jihar a zaben da aka kammala.
Nwauju ya jaddada kudirin jam’iyyar na ba da goyon baya dari bisa dari ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu.
Sai dai sanarwar ta gargadi wadanda suka bayyana a matsayin ‘yan bangar siyasa da su daina al’adar rashin kunya ta amfani da sunan jam’iyyar APC wajen neman tagomashi daga ‘yan siyasa masu ra’ayin rikau da ke neman dacewa a cibiyar.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Kano Ta Sanya Alamar Rushe Wasu Wuraren Kasuwanci
Gwamnatin jihar Kano ta sanya alamar ruguje wasu kadarori da suka hada da filayen ajiyar motoci na miliyoyin Naira da gidajen mai da ke kan babbar hanyar BUK domin rugujewa.
Kadarorin dai wasu ne da aka gina a kusa da tsohuwar katangar ganuwar birnin Kano (Badala) wanda gwamna mai ci Abba Kabir Yusuf ya zargi tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da karkatar da kudaden raya kasa ba bisa ka’ida ba.