“Ba ni da aure, kuma Sam bani neman Aure” – Omah Lay
Shahararren Mawaƙin Najeriya Stanley Omah Didia wanda aka fi sani da Omah-Lay ya ce a halin yanzu bai yi aure ba, shi kadai yake rayuwarsa.
A cewar dan wasan na ‘Boy Alone’ ya daɗe bai yi aure ba amma kuma har yanzu baya neman kowace Mace da niyyar Aure.
Da yake magana a wata hira da ya yi da gidan rediyon The Beat FM da ke ƙasar London wato United Kingdom, Omah Lay ya bayyana cewa yana son ya zauna shi kaɗai ba tare da yayi aure da tsawon wani lokaci domin ya mayar da hankali kan sana’arsa ta waƙa.
Jami’in da ke gabatar da shiri ya tambaye shi “Shin a halin yanzu kana soyayya”?
Omah Lay ya amsa da “A’a”, ina son II n kasance marar aure na tsawon lokaci [na daɗe] kuma ina sonbhakan, ina jin daɗin hakan, kuma ina so in zauna a haka har zuwa tsawon lokacin da Allah ya sanya ko ya tsara Mani.
KARANTA WANNAN LABARIN:“Ku kai rahoton duk wanda kuka gani da harsashi ga Jami’an tsaro”- PRO ya buƙaci yan Najeriya
Ya ƙara da cewa, magoya bayana mata da ke ta ƙoƙarin samun shiga a gare shi a halin yanzu ba za su sami wata amsa mai kyau ba, don haka sai su saurara.
Burna Boy na fi so kaf a cikin Mawaƙan Najeriya – Rotimi Amaechi
Tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana fitaccen Mawaƙin Najeriya da yafi so.
Ya bayyana cewa yana bibiyar Davido, da Wizkid, da Tiwa Savage, amma shi babban masoyin Burna Boy ne saboda salon wakarsa yana birgeshi.
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da Arise TV.
Ya ce wakar da ya fi so a yanzu ita ce ‘Agba Baller’ ta Flavour.
Amaechi ya ce, “A fagen waƙa duk ina bibiyarsu [mawakan Najeriya] ina bin Davido Wizkid Tiwa Savage amma ni babban masoyin Burna Boy ne saboda irin wakokin da yake yi kuma ina sauraren su duka.
Amma babbar waƙarsa da nafi so yanzu ita ce Flavour’s Agba Baller”