Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya shaida wa Sarki Charles III cewa ba shi da gida a Burtaniya a ziyarar da ya kai wa sarkin.
Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa wata tambaya a wani faifan bidiyo mai tsawon dakika 25 da mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Tolu Ogunlesi ya wallafa a shafinsa na Twitter.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Mata Na Fuskantar Zaman Gidan Yari Biyo Bayan Yin Dage-dagen Naman Jemage Tare Da Cinye Shi
Shugaban ya ce, “Lokacin da shi (Sarki Charles III) ya tambaye ni ko ina da gida a nan (Birtaniya), sai na ce a’a, ko a Najeriya, wadanda nake da su su ne wadanda na gina kafin in shiga gwamnati.
“Ba ni da sha’awar samun dukiya a ko’ina. Ina jin ‘yanci lokacin da ba ni da komai,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Barazanar Taro: Za A Gurfanar Da Waɗanda Aka Kama Da Laifi — IGP
Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin yada shawarar tafiye-tafiye da kasashen Amurka da Birtaniya suka bayar a Abuja zuwa kotu.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da jawabi a taron manema labarai na gidan gwamnati da tawagar shugaban kasa kan sadarwa ta shirya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.