- Sabon Ministan da aka rantsar, Nyesom Wike ya taka rawa a ranar da ya fara aiki a babban birnin tarayya.
- Tsohon gwamnan jihar Ribas ya sha alwashin kawo karshen kiwo a fili a Abuja yayin da ya ce zai tuntubi makiyaya
- Wike ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, yayin da ya ci alwashin tsaftace babban birnin tarayya Abuja.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sabon ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya sha alwashin kawo karshen kiwo a fili a cikin Abuja, inda ya ce ba za a iya jurewa irin wannan.
A cikin wani faifan bidiyo da AIT ta wallafa, Wike ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tuntuɓi makiyaya, yana mai cewa, “Ba za mu bar shanu a cikin Abuja ba”.
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, jim kaɗan bayan rantsar da shi, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Keyamo Ya Bukaci Hadin Kan Ma’aikata don Ciyar da Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama Gaba
Jaridar Vanguard ta kuma ƙara da cewa, tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce makiyaya za su iya kiwon shanu a wajen birnin amma kuma ba za a bari su ci ciyawar da ake amfani da ita wajen ƙawata birnin ba .
“Za mu tuntuɓi makiyayan domin mu ga yadda za mu daina (kiwo a fili) saboda ba za mu iya barin shanu a cikin gari ba,” in ji shi a wajen taron da aka yi a unguwar Garki da ke Abuja.
Wike ya kara da cewa:
“Suna iya zama a wajen birnin saboda ciyayi suna wajen birnin. An dasa ciyayi a cikin birnin domin ƙawata birnin. Ba wanda za su ci ba ne.
Kalli bidiyon yayin da Wike ya sha alwashin kawo karshen kiwon shanu a cikin garin Abuja
We will not allow cows inside Abuja – Wike pic.twitter.com/rGVpluPynD
— AIT (@AIT_Online) August 21, 2023
Jam’iyar PDP Ce Tace In Karbi Mukamin Minista-Wike
A wani labarin kuma: Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi ikirarin cewa jam’iyyar PDP ta ba shi damar karbar mukamin minista a karkashin gwamnatin Bola Tinubu.
Wike, wanda ya bayyana shugabannin PDP a matsayin masu rawan reggae da suka yi masa barazanar sanya masa takunkumi, ya ce jam’iyyar ta bashi goyon baya sosai kafin ya karbi mukamin.