Babban mai kula da Cocin Redeemed Christian Church of God, RCCG Fasto E. A Adeboye ya yi gargadi da kakkausar murya ga jama’a da baki game da sanya tufafin da ba su dace ba a sansanin.
Adeboye ya yi wannan gargadin ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mai taimaka wa Janar Oladele Balogun.
Karanta nanWani Sashe Na Jami’ar Ahmadu Bello Dake Zaria Ya Kama Da Wuta
A cewar sanarwar, shugabannin cocin sun kuduri aniyar ladabtar da duk wanda aka samu da laifin karya dokokin da ke jagorantar sansanin.
Sanarwar ta kara da cewa muna so mu sanar da duk mazauna garin Redemption a hukumance cewa, a cikin alƙawarinmu na kiyaye tsarkakakken birnin da kuma ɗaukaka matsayin ‘Birni Mai Tsarki.
Hukumar cocin tana aiwatar da tsauraran matakai game da sanya tufafin da ba su dace ba a duk faɗin birnin.
Birnin Redemption da aka fi sani da Redemption Camp shine babbar harabar na duniya na cocin mega Pentecostal dake cikin jihar Ogun Nigeria.
Birnin Redemption shine inda cocin ke gudanar da taro da shirye-shirye na musamman.
A wani labarin kumaMuna Kan Bakarmu Dangane Da Dakatar Da Kwankwaso-NNPP
Kwamitin zartaswa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a shiyyar Arewa maso Gabas, sun tabbatar da korar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso.
An bayyana hakan ne a cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron zartarwa da masu ruwa da tsaki na yankin Arewa maso Gabas da aka gudanar a Bauchi ranar Juma’a.
Bugu da kari, jam’iyyar NNPP ta arewa maso gabas ta nuna rashin gamsuwarta da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tsige gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf.